‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci, Sun Kashe Masallata 3 Tare da Sace Wasu da Dama a Jihar Arewa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci, Sun Kashe Masallata 3 Tare da Sace Wasu da Dama a Jihar Arewa

  • 'Yan bindiga sun kai kazamin hari yankin Kankara da ke jihar Katsina a daren ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu
  • Wani mazaunin garin ya ce 'yan ta'addan sun kashe mutum uku a lokacin da ake tsaka da gudanar da sallar Isha'i
  • Haka kuma maharan sun jikkata wasu mutum hudu wadanda ke kwance a asibiti yanzu haka, sannan sun sace wasu da dama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Tsageryn 'yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a jihar Katsina a daren ranar Laraba da safiyar Alhamis, inda suka kashe akalla mutane uku tare da sace wasu da dama.

A wani lamari mai firgitarwa yayin sallar Isha'i a daren Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 'yan bindigar sun bude wuta kan bayin Allah da ke sallah, inda suka kashe uku daga cikinsu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

'Yan bindiga sun farmaki masallata a Katsina
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci, Sun Kashe Masallata 3 Tare da Sace Wasu da Dama a Jihar Arewa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Yadda 'yan bindiga suka farmaki masallata a Katsina, majiya

Wata majiya da ta yi bayanin yadda lamarin ya faru ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Makasan sun farmaki 'yan uwanmu Musulmi yayin sallar Ishai. Abun bakin ciki, biyu daga cikinsu sun rasa ransu a cikin harabar masallacin, yayin da mutum na uku ya hadu da ajalinsa a wajen masallacin yayin da yake kokarin tserewa.
"Mutum hudu sun ji rauni kuma yanzu haka suna samun kulawar likitoci a wani asibiti a Kankara."

Haka kuma, majiyar ta bayyana cewa 'yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wani mutum da mata biyu a yayin harin.

"Abin takaici, mutumin ya rasa ransa sakamkon kin bin maharan da ya yi inda suka yi masa datsa-datsa kan ya ki bari masu garkuwan su yi gaba da shi," inji majiyar.

'Yan bindiga sun farmaki gidan 'dan banga

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mahara sun hallaka jami'an 'yan sanda 2 da sace fiye da 40 a sabon hari a Zamfara

A wani lamari na daban, da misalin karfe 2:30 na tsakar daren Alhamis, 'yan bindiga sun farmaki gidan Sani Maikifi, wani 'dan banga a unguwar Tudun Boka a garin Kankara.

Cikin ikon Allah, Sani ya yi nasarar tserewa ta kofar bayansa, inda ya kerewa 'yan bindigar, amma maharan sun tafi da mata da 'dansa, rahoton Daily Post.

Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigar da suka dade suna bibiyar Sani, sun kai farmaki cikin shiru, inda suka kutsa cikin garin Kankara ba tare da tayar da hankali ba.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan kasuwa

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mahara da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka ƴan kasuwa 9 a titin Jibia zuwa Batsari da ke jihar Katsina ranar Lahadi da yamma.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan kasuwan na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Jibia lokacin da suka faɗa tarkon ƴan bindiga da misalin ƙarfe 6:00 na yammaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel