Rashin Tsaro: Tinubu Ya Bayyana Babban Abin da Ya Saka a gaba a Najeriya

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Bayyana Babban Abin da Ya Saka a gaba a Najeriya

  • Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta fifita lamarin tsaron kasa fiye da komai
  • Bola Tinubu ya yaba da kokarin sojoji da sauran hukumomin tsaro a yaki da ‘yan ta’adda da masu aikata sauran laifuffuka
  • A wani bangare kuma, Hafsan Tsaron Najeriya ya jaddada bukatar amfani da sababbin fasahohi don magance matsalolin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sanya tsaron kasa a lamba ta daya a kan komai da komai.

A karkashin haka, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa za a ci gaba da daukar matakai don inganta tsaro a Najeriya.

Tinubu
Tinubu ya fadi matakan da ya dauka na magance matsalar tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin taron hafsoshin tsaro da kwamandojin hadin gwiwa da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ji takaicin konewar almajirai, ya ba da umarnin dakile gobara a tsangayu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin taron, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa kokarin da suke yi don dakile matsalolin tsaro a fadin kasar nan.

Shugaba Tinubu ya yabawa sojoji

A jawabinsa wanda Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya wakilta, shugaba Tinubu ya jinjina wa dakarun tsaron Najeriya bisa jajircewarsu wajen yakar ‘yan ta’adda da sauran miyagu.

"Ina matukar yabawa namijin kokarin dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
"Wannan kokari na su yana da matukar muhimmanci wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba da bunkasa,"

- Bola Tinubu

Ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da goyon baya ga rundunar soji da dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da suna gudanar da ayyukansu ba tare da tangarda ba.

Bukatar hadin gwiwa a fannin tsaro

Shugaba Tinubu ya bukaci hukumomi su hada kai don ganin an kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Na yi kokari': Buhari ya jero bangarorin da ya kawo sauyi a mulkinsa, an yaba masa

Ya ce dole ne hukumomin tsaro su rungumi sababbin dabaru, su kuma yi amfani da fasahar zamani wajen dakile hare-haren ta’addanci.

"Dole ne hukumomin tsaro su hada kai domin yakar ta’addanci da sauran laifuffuka. Ya zama wajibi mu rungumi sababbin fasahohi da dabarun yaki da ‘yan ta’adda.
"Akwai bukatar mu karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin cimma nasara,"

- Bola Tinubu

Shugaban ya bukaci mahalarta taron da su fito da sababbin hanyoyin da za su taimaka wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.

Bayanin hafsan tsaron Najeriya

Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa an samu karuwar amfani da abubuwan fashewa da kuma jiragen yaki marasa matuki a hannun ‘yan ta’adda.

"Dole ne mu tashi tsaye domin dakile wadannan matsaloli. Yadda ‘yan ta’adda ke amfani da sababbin fasahohi na bukatar mu kara kaimi wajen amfani da dabarun zamani.
"Ya zama wajibi mu karfafa hadin gwiwa, mu kuma inganta tsarin tattara bayanan sirri don magance barazanar,"

Kara karanta wannan

"A ajiye duk manufar da za ta wahalar da talaka," Gwamna ya soki tsare tsaren Tinubu

- Janar Christopher Musa

Tinubu ya matsa lamba kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce nan da shekara daya za a shawo kan matsalar tsaro.

Legit ta rahoto cewa ministan ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi inda ya bayyana cewa Bola Tinubu ya matsa musu lamba kan tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng