"A Ajiye duk Manufar da za Ta Wahalar da Talaka," Gwamna Ya Soki Tsare Tsaren Tinubu

"A Ajiye duk Manufar da za Ta Wahalar da Talaka," Gwamna Ya Soki Tsare Tsaren Tinubu

  • Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya soki matakan tattalin arzikin Bola Ahmed Tinubu da suka jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar wahala
  • Gwamnan ya bayyana cewa hauhawar farashi da rashin aikin yi sun haddasa fushi da takaici a tsakanin al'umma, don haka akwai bukatar sauyi
  • Fintiri ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba manufofinta na tattalin arziki domin rage radadin wahala ga ‘yan Najeriya su ke sha
  • Ya ja hankalin gwamnati da kada ta aiwatar da manufofi da za su kara jefa al'umma cikin kunci, yana mai cewa Najeriya kasa ce ta kowa da kowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya caccaki manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya.

Ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke dauka su na jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar wahala.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya soki martanin gwamnatin Abba bayan kisan mutum 4 wajen rusau

Tinubu
Fintiri ya caccaki manufar tattalin arzikin Tinubu Hoto: Ibrahim Mohammed Olajide/Governor Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

A cewar Daily Trust, Fintiri ya bayyana hakan ne a taron shiyyar Arewa Maso Gabas na Kwamitin Sulhu na Kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar a Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“'Yan Najeriya na ji a jikinsu,” Gwamna Fintiri

Gwamnan Adamwa, Ahmadu Fintiri ya caccaki yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zuba ido duk da wahalar da ake sha.

Ya ce:

"Muna wahala. Jama’a su na cikin fushi. kuma manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya ba sa aiki."

Gwamnan ya kara da cewa hauhawar farashi, rashin aikin yi da raguwar ingancin rayuwa ke kara dagula al’amura ga 'yan kasa.

Gwamnan Adamawa, Fintiri ya shawarci Tinubu

Gwamnan ya jaddada bukatar gwamnati ta sauya tsari cikin gaggawa, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake duba manufofinta na gudanar da tattalin arziki.

Ya gargadi cewa ci gaba da aiwatar da manufofin da ba su dace ba zai kara tsananta wahalar da ‘yan kasa ke fuskanta, kuma hakan zai kara yanke kauna tsakanin gwamnati da talakawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sabuwar jami'ar fasaha a Najeriya

Fintiri ya kara da cewa:

"Duk abin da zai sanya mu kuka, bai kamata ya zama bangare na manufarku ba, domin wannan kasa tamu ce."

Gwamna ya soki manufofin gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, ya bi sahun takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, wajen sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Ttarayya.

Gwamna Fintiri ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali kan abubuwan da za su farfado da tattalin arzikin kasa, ba wai kokarin faranta wa IMF da Bankin Duniya ba.

Ya kara da cewa idan da gaske ne gwamnati na son ceto Najeriya daga wannan halin da ake ciki, ya kamata ta gaggauta sauya akalar manufofinta zuwa wadanda za su farfado da tattalin arziki da rayuwar jama’a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.