EFCC: Dattawan Katsina Sun Tunkari Tinubu Gadan Gadan kan Kama Farfesa Yusuf
- Dattawan jihar Katsina sun bukaci a saki tsohon shugaban hukumar inshora ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf ba tare da sharadi ba
- Kungiyar dattawan ta ce Farfesa Usman Yusuf bai aikata wani laifi ba face faɗin gaskiya game da halin da Najeriya ke ciki a yau
- A karkashin haka suka yi kira ga Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya bada ƙarin bayani kan dalilin tsare Farfesa Yusuf
- Wani matashin dan siyasa a jihar Gombe, Bilyaminu Yahaya ya bayyanawa Legit irin tasirin da kama Farfesa Yusuf zai iya yi a kan gwamnati mai ci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Kungiyar dattawan Katsina ta bukaci gwamnatin tarayya da ta saki tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ba tare da wani sharadi ba.
A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Katsina ranar Talata, Sakataren ƙungiyar, Aliyu Muhammad, ya bayyana cewa tsare Farfesa Usman Yusuf abin damuwa ne matuka.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa dattawan sun ce bai kamata a hana Farfesa Yusuf amfani da haƙƙinsa na faɗin albarkacin baki da tsarin mulkin ƙasa ya ba sa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Faɗin gaskiya ba laifi ba ne” – Dattawan Katsina
Sakataren ƙungiyar dattawan Katsina, Aliyu Muhammad ya bayyana cewa:
"Farfesa Usman Yusuf kwararre ne a fannin kimiyyar jinin ɗan Adam da dasa ƙashin mahaifa.
Ya bar aikin da yake yi a Amurka inda yake samun albashi mai tsoka saboda ƙaunar ƙasarsa Najeriya.
Gwamnatin tarayya ce ta nemi ya dawo gida domin taimakawa, inda aka ba shi shugabancin NHIS. Kafin ya samu tangarda a lokacin da ya fara gyara."
Ƙungiyar ta bayyana cewa tsare shi a yanzu ba wani abu bane illa saboda yadda yake bayyana ra’ayinsa a fili a cikin hirarraki da yake yi da kafofin watsa labarai.
Kira ga Bola Tinubu kan Farfesa Yusuf
A yayin taron, tsohon mukaddashin shugaban ƙungiyar, Mamman Danmusa, mai shekaru 82, ya ja hankalin Shugaba Bola Tinubu kan illar da tsare Farfesa Yusuf za ta iya jawowa gwamnatin sa.
Aliyu Muhammad ya ƙara da cewa:
"Muna tunatar da shugaba Tinubu cewa yankin Arewa ne ya ba shi kuri’u fiye da miliyan biyar a zaben da ya kawo shi mulki.
"Yanzu mutane da yawa sun sake sabunta katin zabe saboda halin ƙuncin da muke ciki. Mutane na fuskantar wahala, kuma wannan rashin adalcin ba zai fadi kasa banza ba."
Zargin son kai da rashin adalci
Rahoton Channels ya nuna cewa kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ake nuna son kai wajen magance batutuwan da suka shafi zargin cin hanci da rashawa.
Kungiyar ta ce:
"Akwai mutane da ake zargi da satar biliyoyi da tiriliyoyin Naira amma ba a tsare su ba, amma an kama Usman Yusuf saboda kawai yana faɗin gaskiya."
Dattawan sun yi kira da a saki Farfesa Usman Yusuf domin tabbatar da adalci da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam kamar yadda tsarin mulkin ƙasar nan ya tanada.
A karshe, dattawan Katsina sun ce wata alamar rashin adalci ita ce an zargi Farfesa Yusuf da ba dan uwansa kwangila amma kuma Bola Tinubu ma ya ba dansa kwangila.
Legit ta tattauna da Bilyaminu Yahaya
Wani matashin dan siyasa, Bilyaminu Yahaya ya bayyanawa Legit cewa kama Farfesa Yusuf zai iya kara wa gwamnatin Tinubu bakin jini.
"Idan ka lura da yadda manyan mutane irin su Sheikh Gumi da dattawa Arewa ke nuna bisa zalunci a kama shi, za ka fahimci hakan ya yi tasiri a zukatan 'yan Arewa.
"Hakan zai saukaka mayar da lamarin ya rikide ya dawo siyasa ko da ba da manufar aka kama shi ba."
- Bilyaminu Yahaya
Sheikh Jingir zai gyara hanyar Saminaka
A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kaddamar da gyara hanyar Saminaka zuwa Jos.
Malamin ya kafa gidauniya da za ta gyara hanyar domin jama'a su samu saukin zirga zirga kasancewar titin ya shafe shekaru a lalace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng