Badaƙalar N90m: Laifuffuka 5 da EFCC ke Zargin Tsohon Shugaban NHIS Ya Aikata

Badaƙalar N90m: Laifuffuka 5 da EFCC ke Zargin Tsohon Shugaban NHIS Ya Aikata

  • EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf bisa laifuffuka biyar da suka hada da wawure kudi da bayar da fifiko ba bisa ka’ida ba
  • Ana tuhumarsa da ba wa kamfanonin da ke da alaka da shi kwangiloli, ciki har da sayen mota da horar da mutane ba bisa ka'ida ba
  • Bayan ya musanta laifuffukan, kotu ta dage shari’a zuwa 12 ga Fabrairu, 2025, kuma ta umarci a tsare Usman Yusuf a kurkukun Kuje

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Litinin, 3 ga Fabrairu, 2025, EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, a gaban Mai shari’a Chinyere E. Nwecheonwu.

An gurfanar da shi ne a babbar kotun birnin tarayya da ke Kuchiako Kuje, inda ake tuhumarsa da aikata almundahana da almubazzaranci da kudi.

Kara karanta wannan

Yayin da aka aika Farfesa Usman kurkuku, kotu ta wanke Femi Fani Kayode

EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yahaya kan tuhume-tuhume biyar
EFCC ta yi bayanin wasu daga cikin tuhume-tuhumen da take yiwa Farfesa Usman Yahaya. Hoto: @nhia_nigeria
Asali: Twitter

A rahoton da ta fitar a shafinta na Facebook, EFCC ta ce ana tuhumar Usman da laifuffuka biyar da suka hada da wawure kudi, damfara, da bayar da fifiko ba bisa ka’ida ba, na kudin da suka kai N90,439,178.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta yi bayanin wasu daga cikin tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon shugaban hukumar ta NHIS.

EFCC na zargin Usman ya wawure N19,197,750

Tuhuma ta farko ta ce Farfesa Usman Yusuf, tsakanin 2016 da Yuli 2017, yana matsayin shugaba na NHIS, ya yi amfani da mukaminsa ba daidai ba.

Ana zargin ya amince da sayen mota ga kansa kan N49,197,750 wanda ya wuce kasafin da aka ware na N30,000,000 da babbar riba.

Wannan aiki laifi ne da ya saba da Sashe na 22 na Dokar ICPC ta 2000, wacce ke bayani kan hukunci ga irin wannan saba wa doka.

EFCC na tuhumar Usman da ba GK Kanki fifiko

Kara karanta wannan

'Ya ci kudin alhazai': EFCC ta cafke dan kasuwa a Gombe kan zargin damfarar N144m

Tuhuma ta biyu ta ce Farfesa Usman Yusuf, tsakanin 2016 da 2017, yana NHIS, ya mallaki bukatar kashin kansa a GK Kanki Foundation.

Ba tare da bin ka’ida ba, ana zargin ya ba wa GK Kanki Foundation kwangilar horar da mutane 90 kan N10,100,000, amma 45 aka horas.

Wannan aiki ya saba da Sashe na 22 na Dokar ICPC ta 2000, wacce ke hukunta laifukan da suka shafi cin hanci da saba wa ka’ida.

EFCC na tuhumar Usman da ba Lubekh fifiko

Tuhuma ta hudu ta ce Farfesa Usman Yusuf, tsakanin 2016 da 2017, yana NHIS, ya yi amfani da matsayinsa don amfanuwa da kansa.

Ana zargin ya ba Lubekh Nigeria Limited, mallakin dan uwansa Khalifa Hassan Yusuf, kwangilar N17,500,000 na ayyukan hulda da jama’a.

Wannan aiki ma laifi ne da ya saba da Sashe na 22 na Dokar ICPC ta 2000, wacce ke hukunta almundahana da cin hanci a ofis.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba da sabon umarni kan tuhumar da EFCC ke yi wa tsohon shugaban NHIS

Kotu ta garkame Usman a gidan yarin Kuje

A wani labarin, mun ruwaito cewa Farfesa Usman Yusuf ya musanta dukkanin tuhumomin da hukumar ke yi masa tare da rokon kotu ta tsare shi a hannun EFCC.

A hukuncinta, Mai Shari’a Nwecheonwu ta dage shari’ar zuwa ranar 12 ga Fabrairu, 2025, don sauraron bukatar belin Usman, tare da tsare shi a kurkukun Kuje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.