"Akwai Matsala": Majalisar Amintattun PDP Ta Shiga Taron Gaggawa a Abuja
- Bayan rikicin da ya faru har aka ba hammata iska a makon jiya, majalisar amintattun PDP watau BoT ta kira taron gaggawa a Abuja
- An ruwaito cewa taron na yau Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025 na gudana ne a wani otal da ke birnin tarayya Abuja
- Shugaban BoT, Sanata Adolphus Wabara, da sakatarensa, Ahmed Maƙarfi duk halarci taron wanda zai duba rigingimun da suka addabi PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar amintattu na jam'iyyar PDP ta ƙasa (PDP-BoT) ta shiga taron gaggawa a Transcorp Hilton Hotel da ke cikin ɓabban birnin tarayya Abuja.
BoT ta shirya wannan zama yau Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025 domin tattaunawa da nemo mafita kan rikicin cikin gida da ke addabar PDP.

Asali: Facebook
Vanguard ta ruwaito cewa taron zai maida hankali ne kan matsalolin da suka taso daga hukuncin kotuna daban-daban kan rigimar kujerar sakataren PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan
"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rigima ta kaurewa PDP a taron BoT
Idan za ku iya tunawa a taron BoT da ya gabata a makon jiya, an yi rikici mai zafi har da doke-doke tsakanin ɓangarori biyu masu rigima kan kujerar sakatare.
Lamarin ya faru ne lokacin da Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye suka isa hedkwatar PDP ta ƙasa domin halartar taron BoT.
Kowane daga cikinsu ya halarci taron ne a matsayin sakataren PDP, lamarin da ya haifar ɗa hayaniya har sai da jami'an tsaro suka ashiga tsakani.
Majalisar Amintattun PDP ta kira taron gaggawa
A halin yanzu, Majalisar amintattu ta sake shirya taro wanda ke gudana yanzu haka amma a ba a hedkwatar PDP ta ƙasa ba
A taron BoT na yau Laraba, ana sa ran ƴan Majalisar za su duba halin da PDP ta tsinci kanta da kuma lalubo hanyar warware duk wani rikici cikin ruwan sanyi.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugaban BoT, Sanata Adolphus Wabara, sakataren, Sanata Ahmed Maƙarfi, tsofaffin gwamnoni; Achike Udenwa, Sam Egwu da Babangida Aliyu
Sauran waɗanda aka hanga sun shiga taron sune Sanata Ben Obi da kuma Cif Olagunsoye Oyinlola, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Abubuwan da BoT za ta tattauna
Ana sa ran taron zai tattauna yadda za a daidaita rikicin cikin gida da ke hana jam’iyyar ci gaba, tare da duba hanyoyin farfado da martabar PDP a fagen siyasa.
Baya ga batun shugabanci, ƴan BoT za kuma su yi nazarin hanyoyin hada kai domin karfafa jam’iyyar gabanin babban zabe mai zuwa a 2027.
An tattaro cewa da yiwuwar taron zai samar da matsaya da za ta kai ga warware sabanin da ke tsakanin bangarorin PDP damon tunkarar kalubalen siyasa a nan gaba.
Rikici na neman kara ɓallewa a PDP
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Samuel Anyanwu ya sha alwashin sa ƙafar wando ɗaya da duk wanda ya yi yunƙurin tsige shi daga kujerar sakataren PDP.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
Anyanwu ya bayyana haka ne da yake martani ga matakin gwamnonin PDP, waɗanda suka ayyana Sunday Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakatare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng