Abin da Kashim Shettima Ya Ce kan Bikin Maulidi a Kano Duk da Zargin Kokarin Hana Taron

Abin da Kashim Shettima Ya Ce kan Bikin Maulidi a Kano Duk da Zargin Kokarin Hana Taron

  • Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba wa darikar Tijjaniyya kan kokarinta na hada kan Musulmai tare da ciyar da zaman lafiya gaba a Najeriya
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ma ya jinjina wa darikar saboda yadda suka kasance ginshiki wajen tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin al'ummomi a kasar
  • A bangarensa, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi addu'a ga zaman lafiya da hadin kai tsakanin Musulmai da mutunta mabiyan sauran addinai a duniya baki daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da rawar da darikar Tijjaniyya ke takawa wajen hada kan al’ummar Musulmi a Najeriya.

Shettima ya yi wannan jawabi ne yayin bikin Maulidi na 2025 domin tunawa da marigayi Sheikh Ibrahim Niass.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Shettima ya yaba wa darikar Tijjaniya kan dogewa a zaman lafiya
Kashim Shettima ya bayyana gudunmawar da darikar Tijjaniya ke bayarwa wurin zaman lafiya. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Yan sanda sun tura jami'ai taron Maulidi

Mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir, Sanusi Bature shi ya bayyana haka a yau Adabar 25 ga watan Janairun 2025 a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan matakin rundunar 'yan sandan Kano na janye matakin hana Mauludin Tijjaniyya bayan takaddama mai karfi da gwamnatin jihar ta yi kan lamarin.

Gwamnatin Kano ta zargi 'yan sanda da yunkurin hana taron shekara-shekara da ake shiryawa tun shekaru 39 da suka gabata.

Rundunar 'yan sanda ta gargadi jama’a game da wasu barayi da ke fakewa da aikin cajin wayoyin salula domin aikata sata a wurin taron.

Musabbabin gudanar da bikin duk shekara a Kano

Sanusi Bature ya ce an gudanar da bikin ne domin tunawa da Sheikh Ibrahim Nyass a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Sanarwa ta ce Shettima, wanda Alhaji Babagana Fannami ya wakilta, ya jinjina wa darikar kan bin koyarwar addinin Musulunci tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida ya jawo hadimin Kwankwaso, ya nada shi a Mukami

Shettima, wanda ya kasance babban bako a taron, ya yaba wa koyarwar darikar Sufi da aka sani da jaddada taimakon bil’adama.

Babban baƙon ya jaddada tsayin dakan darikar Tijjaniyya wajen bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW) tare da gujewa sabanin fahimtar addinin Musulunci.

Ya kuma tunatar da Musulmai su yi koyi da koyarwar gaskiya ta addinin Musulunci tare da gujewa tsattsauran ra’ayi.

Gwamna Abba Kabir ya yi tsokaci kan bikin

A martaninsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa kokarin darikar Tijjaniyya wajen samar da zaman lafiya da kyakkyawar dangantaka tsakanin dariku a Najeriya.

“A matsayina na mai masaukin baki, ina gode muku duka da kuka halarci wannan bikin Mauludi na shekara-shekara na Sheikh Ibrahim Niass daga ko’ina.”

- Abba Kabir Yusuf

Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne jagoran darikar Tijjaniyya na kasa, ya yi addu’ar samun hadin kai da zaman lafiya tsakanin Musulmai da mutunta mabiyan sauran addinai a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Abba Kabir ya halarci bikin Maulidi a Kano

A baya, kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa al'ummar jihar Kano sun yaba da kokari da jarircewar gwamnan wajen tabbatar da an yi taron.

Gwamnan ya yaba wa kokarin Tijjaniyya karkashin jagorancin Khalifa Muhammad Sanusi II wajen samar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.