A Karshe, An Bayyana Kudin Kujerar Aikin Hajjin 2024, Musulman Arewa Za Su Biya N8.4m

A Karshe, An Bayyana Kudin Kujerar Aikin Hajjin 2024, Musulman Arewa Za Su Biya N8.4m

  • NAHCON ta sanar da cewa an yanke Naira miliyan 8.7 a matsayin kudin kujerar aikin Hajin shekarar 2025 ga maniyyata daga Kudu
  • Shugaban NAHCON, Abdullahi Usman, ya ce maniyyata daga Arewacin kasar nan ba za su biya kudin da ya kai na 'yan Kudu ba
  • Hukumar ta bukaci maniyyata aikin Hajjin 2025 da su bi dokokin Saudiyya, su yi rajista da biyan kudi da wuri don gujewa matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta amince da Naira miliyan 8.7 a matsayin kudin aikin Hajjin 2025 ga maniyyata daga kudancin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NAHCON ta yi nuni da cewa maniyyata daga jihohin Arewa maso Gabas za su biya kasa da Naira miliyan 8.7.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Hukumar NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin Hajjin 2024 a Najeriya
Kudin kujerar aikin Hajjin 2025 ya haura N8m, NAHCON ta yi karin bayani. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

NAHCON ta sanar da kudin aikin Hajjin 2025

Sanarwar da aka wallafa a shafin NAHCON na X ta ce maniyya daga jihohin Borno da Adamawa, za su biya N8,327,125.59.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta kuma ce maniyyata daga sauran jihohin Arewacin Najeriya za su biya N8,457,685.59 yayin da na Kudancin kasar za su biya N8,784,085.59.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da Fatima Usara, daraktar watsa labaran hukumar ta fitar a ranar Litinin, 20 ga Janairu.

Gwamnatin Tinubu ta amince da kudin Hajjin 2025

Farfesa Abdullahi ya ce an yanke kudin da alhazan za su biya bayan tarurrukan hadin gwiwa mai yawa da aka gudanar tsakanin masu ruwa da tsaki.

Shugaban na NAHCON ya gode wa ofishin shugaban kasa da kungiyar sakatarorin jin dadin alhazai na jihohi bisa goyon bayan da suka bayar.

Kudin aikin Hajjin 2025 ya samu amincewar ofishin mataimakin shugaban kasar Najeriya, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Abin da sanarwar NAHCON ke cewa

Sanarwar hukumar ta ce:

"Alhazai daga yankin Borno da Adamawa za su biya Naira miliyan 8.33 a hajjin 2025.
"A Kudancin Najeriya, kudin aikin hajji zai kai Naira miliyan 8.78, yayin da alhazai daga Arewa za su biya Naira miliyan 8.46."

Shugaban ya bayyana cewa NAHCON tare da Malam Ameen Amshi, wakili na musamman ga shugaban kasa, sun yi kokarin samun rangwame a farashin hajjin.

"An cimma wannan farashin ne bayan shawarwari masu yawa domin tabbatar da adalci da shiga tsakani wajen yanke kudin."

Shugaban ya yi kira ga alhazai su bi dokokin Saudiyya da su yi rajista da biyan kudi da wuri don guje wa matsaloli.

An fadi kudin aikin Hajjin 2024

Idan ba a manta ba, a 2024, Legit Hausa ta rahoto cewa hukumar NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin Hajjin 2024, inda za a biya Naira miliyan 4.9.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Duk da ragin da aka sanar da samu, hukumar ta bayyana wannan farashi a matsayin kudin kujerar aikin hajji ga maniyyata daga Kudancin kasar nan.

A baya, NAHCON ta ayyana biyan Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya, wanda mafi yawan maniyyata ba su iya biyan wannan kudin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.