"Ba Tinubu Ya Tura Ni ba": Obasanjo Ya Fadi Dalilin ba da Shaida a Kotun Faransa
- Shugaba Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba wanda ya tura shi bayar da shaida kan rikicin kwangilar Mambilla a Paris
- Obasanjo ya ce ya yanke shawarar bayar da shaida ne domin gyara wasu bayanai da tsohon ministan wuta, Olu Agunloye, ya fada
- Kamfanin Sunrise Power yana neman diyyar $2.3bn daga Najeriya, inda ya zargi kasar da karya yarjejeniyar aikin tashar wutar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilinsa na bayar da shaida kan rikicin shari’ar aikin wutar lantarkin Mambilla a kasar Faransa.
Obasanjo ya bayar da shaida a ranar Laraba, yayin da shima tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga ya bayar da tasa shaidar.

Asali: Getty Images
Obasanjo ya magantu kan ba da shaida a Faransa
Bayanin Obasanjo na zuwa ne a matsayin martani ga masu yada jita-jitar cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya turasa Farasan don ba da shaida, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya ce:
"Ni ne na ga damar gabatar da kaina don bayar da shaida kan wannan lamarin. Babu wanda ya sanya ni. Shugaba Tinubu bai aike ni ba, sabanin jita-jitar da ake yadawa."
Obasanjo ya ce ko da ya shirya zuwa bayar da shaidar, bai sanar da kowa ba, don haka zancen 'wai' wani ne ya sanya shi ba gaskiya ba ne.
Dalilin zuwan Obasanjo Faransa ba da shaida
Kusa a Najeriya, ya ci gaba da cewa:
“Na yanke shawarar bayar da shaida ne saboda kalaman da Olu Agunloye ya yi kan lamarin. Na yi nazari kan kalamansa marasa tushe, shi ya sa na ga ya dace na fito da gaskiya."
Kamfanin Sunrise Power, wanda aka ba kwangilar gina aikin lantarkin a 2003, yana karar Najeriya a gaban kotun kasuwanci ta Duniya a Faransa.
Kamfanin yana zargin gwamnatin Najeriya da karya yarjejeniya, tare da neman diyyar dala biliyan 2.3 domin abin da suka kashe kan kwangilar.
To sai dai Olu Agunloye (tsohon ministan wuta) da ake zargi da laifi a lalacewar kwangilar, ya ce Obasanjo ne ya amince da kwangilar tun kafin ma ya zama minista.
Wannan batu da Agunloye ya yi, ya sa Obasanjo ya ce ya fito domin warware rudanin da aka samu game da batun kwangilar wutar Mambila.
Takaddamar Obasanjo da Agunloye
Obasanjo ya fara dora alhakin gazawar aikin wutar Mambilla kan Agunloye, yana zarginsa da yin sakaci wajen tafiyar da aikin tsakanin 1999 da 2003.
Amma a wajejen shekarar 2023, Agunloye ya musanta zargin Obasanjo, yana mai cewa tsohon shugaban ya san da yarjejeniyar tun da shi ne ya amince da ita.
Shi ma Obasanjo ya karyata kalaman Agunloye, inda ya bayyanawa duniya cewa bai bayar da izini ba da kwangilar tashar Mambilla ga Sunrise Power ba.

Kara karanta wannan
'Neman gwamna ba zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da aka tsige ya fadi dalilin taso shi a gaba
Obasanjo, Buhari sun ba da shaida a Faransa
Tun da fari, mun ruwaito cewa rigimar kwangilar Mambilla tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Sunrise Power ta kai gaban kotun kasuwanci a Faransa.
Tsoffin shugabannin kasa, Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo, za su bayar da shaida kan rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.
Obasanjo da Buhari sun bar Najeriya zuwa Faransa domin halartar shari'ar, inda kamfanin ke neman diyya daga gwamnatin Najeriya.
Asali: Legit.ng