Babban Magana: Obasanjo Ya Nemi Bayar da Shaida Kan Tsohon Ministan da EFCC Ke Nema Ruwa a Jallo

Babban Magana: Obasanjo Ya Nemi Bayar da Shaida Kan Tsohon Ministan da EFCC Ke Nema Ruwa a Jallo

  • A ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, EFCC ta ayyana neman wani tsohon ministan Najeriya, Olu Agunloye ruwa a jallo kan badakalar kudi dala biliyan 6
  • Agunloye wanda ya yi aiki karkashin gwamnatin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin dan majalisa yana da shari'a da hukumar yaki da rashawa
  • Yanzu haka, Obasanjo ya tsoma baki a lamarin tare da bayyana aniyarsa na bayar da shaida a kan dan siyasar na Ondo

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sanar da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu cewa a shirye yake ya bayar da shaida kan tsohon ministan makamashi da karafa, Olu Agunloye wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin rashawa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya nada tsohon soja a matsayin shugaban hukumar Hisbah, ya fadi dalili

Obasanjo ya kasance shugaban kasar Najeriya tsakanin 1999 da 2007, kuma a karkashinsa ne Agunloye ya yi aiki a matsayin ministan makamashi da karafa tsakanin 1999 da 2003.

Obasanjo zai ba da shaida kan Agunloye
Babban Magana: Obasanjo Ya Nemi Bayar da Shaida Kan Tsohon Ministan da EFCC Ke Nema Ruwa a Jallo Hoto: Mfoniso Rufus, Olu Agunloye
Asali: Facebook

Obasanjo ya caccaki Olu Agunloye

Ku tuna cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Hana Yiwa Tttalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta ayyana neman Agunloye ruwa a jallo kan rawar ganin da ya taka a kwangilar $6bn domin aikin wutar Mambilla.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ne ya ayyana hakan a cikin wata sanarwa a fadin dandalin soshiyal midiya na hukumar a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba.

A wani rahoton The Cable, Obasanjo ya jaddada cewa babu ministan da ke da ikon amincewa da kudin da suka wuce naira miliyan 25 ba tare da yardar Shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: EFCC ta fara neman tsohon minista Agunloye ruwa a jallo, ta fadi dalili

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa Obasanjo ya ba Lateef Fagbemi, atoni janar kuma ministan shari'a, tabbacin ci gaba da taimakawa gwamnatin "ta hanyar yin karin haske kan wannan lamari kamar yadda ake bukata a gare ni."

Obasanjo ya dage kan cewa Agunloye ya aikata “zamba, yaudara, da rashin gaskiya”, inda ya kara da cewa “irinsa ba su da wani amfani ga Najeriya da yan Najeriya”.

Jaridar ta nakalto Obasanjo yana cewa:

"Na yanke shawarar gabatar da kaina don bayar da shaida ta kowani kafa da zai dace da ra'ayin kasarmu."

EFCC na neman Agunloye ido rufe

A baya mun ji cewa hukumar da yaki da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) ta ayyana Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi da karafa matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan zargin rashawa.

Agunloye ya rike mukamin minista karkashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel