Obasanjo Ya Yi Magana Kan Badakalar Kwangilar Wutar Mambila Ta $6bn

Obasanjo Ya Yi Magana Kan Badakalar Kwangilar Wutar Mambila Ta $6bn

  • Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya musanta amincewa da bayar da kwangilar $6bn domin aikin wutar Mambilla a shekarar 2003
  • Obasanjo ya ƙaƙubalanci Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi da ƙarafa ya bayyana wanda ya sanya shi bayar da kwangilar
  • Tsohon shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ministoci a ƙarƙashin mulkinsa ba su da hurumin amincewa da sama da N25m ba tare da izninsa ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bai taɓa amincewa da bayar da kwangilar $6bn ga kamfanin Sunrise Power and Transmission Ltd dangane da aikin samar da wutar Mambilla a shekarar 2003.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da jaridar TheCable wacce aka wallafa a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

"Yadda Na Yi Kwamishina, Minista Ba Tare Da NYSC Satifiket Ba": Na Hannun Daman Buhari Ya Fasa Kwai

Obasanjo ya yi magana kan kwangilar Mambilla
Obasanjo ya ce bai taba amincewa da kwangilar $6bn ta wutar Mambilla ba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon ministan ya ƙalubalanci Olu Agunloye, tsohon ministan makamashi da ƙarfa, ya gayawa ƴan Najeriya inda ya samu iznin bayar da kwangilar ta $6bn.

Ba ministan da ke iznin amincewa da sama da N25m a gwamnatina, Obasanjo

Da yake musanta cewa ba shi ba ne ya ba Agunloye umarnin shigar da Najeriya cikin kwangilar ta $6bn ba, Obasanjo ya bayyana cewa babu ministan da a ƙarƙashinsa ya ke da ikon amincewa da kuɗin da suka wuce N25m.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Lokacin da na ke shugaban ƙasa, babu ministan da ya ke da hurumin amincewa da kuɗin da suka wuce N25m ba tare da amincewar shugaban ƙasa ba."
"Ba zai taɓa yiwuwa ba Agunloye ya shigar da gwamnatina cikin kwangilar $6bn ba tare da izni na ba, kuma ban ba shi wannan iznin ba."

Kara karanta wannan

DSS Ta Kara Fadada Bincike Kan Emefiele, Ta Sake Titsiye Wani Mataimakin Gwamnan CBN

Wutar Mambilla: A shirye na ke na bayar da shaida, Obasanjo

Obasanjo wanda ya ƙalubalanci Agunloye ya yi bayanin inda ya samu iznin bayar da kwangilar, ya ce a shirye ya ke ya bayar da shaida idan gwamnatin Shugaba Tinubu ta kafa kwamitin bincike.

"Idan aka kafa kwamitin bincike a yau domin bincike kan lamarin, a shirya na ke na bayar da shaida. Bana buƙatar ma na bayar da shaida saboda dukkanin takardun suna nan. Ban taɓa amincewa da ita ba." A cewarsa.

Tsohon Sanata Ya Caccaki Atiku

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Oyo ta Kudu ya caccaki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP kan ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

Rilwan Akanbi ya bayyana cewa bai kamata Atiku ya manta da abokantakar da ke tsakaninsa da Tinubu, wajen cigaba da ganin sai ya ɓata sunansa a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel