Badakalar $6bn: Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Obasanjo Gidan Gyaran Hali

Badakalar $6bn: Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Obasanjo Gidan Gyaran Hali

  • Kotu ta garkame tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye a gidan gyaran hali na kuje bayan da EFCC ta gurfanar da shi
  • EFCC na binciken Agunloye kan kwangilar wutar lantarki ta Mambilla da kudinta ya haura dala biliyan 6
  • Tun a watan Disamne ne hukumar ta ayyana Agunloye matsayin wanda take nema ruwa a jallo, inda daga baya ya mika kansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar EFCC, ta gurfanar da Olu Agunloye, tsohon ministan wutar lantarki da karafa, a gaban kuliya bisa zarginsa da aikata zamba.

EFCC na binciken Agunloye kan kwangilar wutar lantarkin Mambilla da kudinta ya haura dala biliyan 6.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta dauki mataki kan dan daba da ya kashe limami, ta kuma hada da mahaifinsa

Kotu ta garkame Olu Agunloye a gidan yarin Kuje
Badakalar $6Bn: ta garkame tsohon ministan Najeriya, Olu Agunloye a gidan gyaran hali na Kuje. Hoto Olu Agunloye
Asali: Twitter

An gurfanar da Agunloye a gaban Donatus Okorowo, alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba inda ya ki amsa tuhumar da ake masa, The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin badakalar wutar Mambila, kotu ta fara hukunci

Vanguard ta ruwaito cewa an tsare tsohon ministan a gidan yarin Kuje har sai ya kammala cika sharuddan belin.

A ranar 13 ga watan Disamba ne hukumar EFCC ta bayyana Agunloye wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahana.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta bukaci jama’a da su bata bayanai masu amfani game da inda Agunloye yake idan sun hadu da shi.

Daga baya ne, wata majiya mai zaman kanta ta sanar da The Cable cewa Agunloye ya mika kansa ga hukumar bayan an fara nemansa.

Kara karanta wannan

Ministar da aka dakatar, Betta Edu ta shiga hannun hukumar EFCC

Gwamnan Anambra ya dakatar da basarake saboda nasa sanata sarauta

A wani labarin, gwamnatin jihar Anambra ta sanar da dakatar da Sarkin Neni, Damian Ezeani bisa kama shi da laifin karya wata doka ta masarautun gargajiya na jihar.

An ruwaito cewa Sarki Ezeani ya nasa Sanata Ubah sarautar 'Odenjinji Neni' abin da gwamnatin ta kalla matsayin karya doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel