Abu Ya Girma: Buhari da Obasanjo Za Su ba da Shaida a Kotun Duniya kan Aikin Mambilla

Abu Ya Girma: Buhari da Obasanjo Za Su ba da Shaida a Kotun Duniya kan Aikin Mambilla

  • Batun rigimar kwangilar Mambilla tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Sunrise Power ya kai gaban kotu kasuwanci da ke Faransa
  • Muhamamdu Buhari da Olusegun Obasanjo za su ba da shaida a gaban kotun kan shari'ar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu
  • Dukkanin tsofaffin shugabannin ƙasan guda biyu sun bar Najeriya domin zuwa ba da shaida a shari'ar ta neman diyya da kamfanin yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsofaffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, za su bayar da shaida a gaban kotun kasuwanci ta duniya (ICC) da ke birnin Paris na ƙasar Faransa.

Tsofaffin shugabannin za su bayar da shaidar ne dangane da ƙarar da kamfanin Sunrise ya shigar da gwamnatin Najeriya, inda yake neman diyyar dala biliyan 2.3 saboda zargin karya yarjejeniyar da suka ƙulla a shekarar 2003.

Kara karanta wannan

Bincike ya fallasa yadda 'yan majalisa ke tilasta wa jami'o'i biyan rashawa

Buhari da Obasanjo za su ba da shaida a kotu
Buhari da Obasanjo za su ba da shaida a gaban kotu kan shari'ar Mambilla Hoto: @BuhariSallau1, @Oolusegun_obj
Asali: Twitter

Majiyoyi sun tabbatarwa jaridar Daily Trust cewa dukkanin tsofaffin shugabannin ƙasan guda biyu suna Faransa dangane da wannan batu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari, Obasanjo za su ba da shaida a kotu

Jaridar TheCable ta rahoto cewa Muhammadu Buhari zai ba da shaidar ne a ranar Litinin, 20 ga watan Janairun 2024.

A ranar Asabar da ta gabata, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya musanta rahotannin da ke cewa an tilastawa wasu manyan ƴan Najeriya bayar da shaida a shari'ar da ke gudana a Paris.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa dukkanin masu bayar da shaidar, suna yi ne a bisa ƙashin kansu da kuma kishin da suke yi wa ƙasarsu.

Kehinde Akinyemi, mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Obasanjo, ya tabbatar da cewa maigidansa yana Faransa a halin yanzu.

Sai dai, ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan ainihin abin da tsohon shugaban ƙasan ya je yi a ƙasar Faransa.

Kara karanta wannan

"Gidaje 3 na mallaka": Buhari ya fadi inda yake samun kudi bayan sauka daga mulki

“Ina iya tabbatar muku cewa tsohon shugaban ƙasan yana Faransa a yanzu, wannan shi ne kaɗai abin da na sani."

- Kehinde Akinyemi

Kokarin jin ta bakin Malam Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, ya ci tura saboda ba a same shi a waya ba har da WhatsApp.

Duk da haka, wasu majiyoyi sun tabbatar cewa Buhari ya bar Najeriya, amma ba a tabbatar da ko yana Faransa ko wata ƙasa ba.

Yaushe aka fara shari'ar?

A ranar 10 ga watan Oktoba, 2017, kamfanin Sunrise Power ya fara shari’ar neman diyyar dala biliyan $2.354 a gaban kotun ICC da ke Paris.

Kamfanin ya shigar da ƙarar ne saboda zargin karya yarjejeniyar gina tashar samar da wutar lantarki mai karfin 3,050MW a Mambilla, jihar Taraba, a tsarin “ginawa, sarrafawa da miƙawa gwamnati” kan kuɗi $6bn.

A wata shari’a ta biyu, kamfanin yana neman biyan diyyar dala miliyan $400 saboda gwamnatin Najeriya ta kasa cika yarjejeniyar sulhu da suka ƙulla a shekarar 2020 don kawo ƙarshen rigimar.

Kara karanta wannan

Buhari, Radda da manyan 'yan siyasa sun yi taron neman nasara ga APC

A wata hira da aka yi da shi a shekarar 2023, Obasanjo ya ƙalubalanci tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye, da ya bayyanawa ƴan Najeriya inda ya samu ikon ba kamfanin Sunrise wannan kwangila a 2003.

Buhari ya yi alhini kan hatsarin Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi alhini kan iftila'in fashewar tankar mai da ya auku a jihar Neja.

Tsohon shugaban ƙasa wanda ya nuna takaicinsa kan lamarin ya yi ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a mummunan hatsarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng