'Yan Bindiga Sun Addabi Gari a Kaduna, Sun Tursasawa Mutane 500 Gudun Hijira

'Yan Bindiga Sun Addabi Gari a Kaduna, Sun Tursasawa Mutane 500 Gudun Hijira

  • Shugaban CDA a karamar hukumar Kauru ya ce mutane 500 ne suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga
  • Abel Adamu ya nemi gwamnati ta kafa sansanonin soja biyu a masarautun Kauru da Kumana don tabbatar da tsaron jama’a
  • Shugaban al'ummar a Kaduna ya ce tattalin arzikin Kauru ya tabarbare saboda hare-haren, wanda ya tilasta mutane yin hijira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Shugaban kungiyar raya al’ummar karamar hukumar Kauru, Abel Adamu, ya bayyana cewa mutane fiye da 500 sun tsere sun bar gidajensu.

Abel Adamu, ya sanar da cvewa hare-haren 'yan ta'adda a Kaurun jihar Kaduna ya tilasta mutane gudun hijira da jawo tabarbarewar tattalin arziki.

Shugaban hukumar CDA ya fadi yadda 'yan ta'adda suka daidaita mazauna Karu, a Kaduna
'Yan bindiga sun tilasta mazauna Kauru, karamar hukuma a Kaduna tserewa daga gidajensu. Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Mazauna Kaduna sun tsere daga gidajensu

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin taron manema labarai a Kaduna, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke kokawa kan yawaitar masu garkuwa da mutane a Kauru, Abel Adamu ya kuma ce mutane da dama sun mutu, wasu sun rasa dukiyoyinsu a hare-haren 'yan ta'addan.

Ya tuna cewa a ranar Juma’ar da ta gabata, an kashe wata mata a Kiffin Chawai bayan ta biya kudin fansa da ‘yan bindigar suka nema.

'Yan bindiga sun kashe wata mata a Kaduna

Adamu ya ce hare-haren sun tilastawa daruruwan mutane barin yankunan Kumana da Kauru, inda suka tsere zuwa wurare daban-daban don tsira da rayukansu.

Yankunan da aka fi kai hare-haren sun hada da Dokan Karji, Bandi, Rumaya, Kwassam, Kaibi, Kusheka, Geshere, da Binawa, inda aka rasa dukiya mai tarin yawa.

"Wannan lamari ya yi muni matuka, don haka muke rokon gwamnati ta dauki matakin gaggawa don tabbatar da tsaro a yankinmu," inji Abel Adamu.

Matsalar tsaro ta tabarbare a yankin Kauru

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

Rahotanni sun bayyana cewa karamar hukumar Kauru, wacce aka fi sani da noma, yanzu ta zama sansanin ‘yan bindiga da ya jefa tattalin arziki cikin matsala.

Abel Adamu ya ce hare-haren baya-bayan nan sun kara nuna tabarbarewar tsaro a yankin, inda jama’a ke cikin fargaba da zaman dar-dar a kullum.

Ya bayyana cewa al’umma sun yi kokarin magance matsalar ta hanyar kafa jami'an sintiri da 'yan banga na cikin unguwanni.

Duk da haka, ya ce yanayin tsaron ya tabarbare matuka, wanda ya sa suke neman gaggawar taimakon hukumomin tsaro da ma na duniya baki daya.

An roki gwamnati ta kafa sansanin soji a Kauru

Don magance matsalar, ya bukaci gwamnati ta kafa sansanonin soji guda biyu, daya a masarautar Kauru, daya kuma a Kumana.

Abel Adamu ya ce sansanonin sojin za su samar da tsaro a yankin, su kuma rage yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar yankin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta'addanci a Kano, an gano wasu bayanai

Shugaban kungiyar ya kuma yi godiya ga gwamnati bisa kafa sansanin soja a masarautar Chawai, tare da neman karin jami’an tsaro don magance hare-haren da ake fuskanta.

'Yan bindiga sun sace basarake a Kauru

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Ungwan Babangida, ƙaramar hukumar Kauru, jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane 15.

Shugaban matasan Kauru, Aminu Khalid, ya bayyana cewa Magajin garin na daga cikin waɗanda aka sace a ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, 2024.

Ya roki gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su kara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga da ke addabar yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.