Yan Sanda Sun Yi Gargadin Yiwuwar Kai Harin Ta'addanci a Kano, an Gano Wasu Bayanai
- Rundunar ‘yan Sanda a Kano ta bayyana cewa ta samu rahoton sirri kan wasu ‘yan ta’adda da ake zargi suna shirin kai hari sassan jihar
- Jami'in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bukaci mazauna Kano su guji wuraren da ke da cunkoso
- SP Kiyawa ya tabbatar da cewa rundunar ta dauki matakan tsaro ta hanyar tura ƙwararru daga sassan kula da abubwan fashewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro ta samu rahoton sirri kan wasu ‘yan ta’adda da ake zargi suna shirin kai hare-hare a jihar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana haka a ranar Juma'a, inda ya ce ana shirin kai hare-haren muhimman wurare da jama'a ke taruwa.

Asali: Facebook
A zantawarsa da Legit, SP Kiyawa ya tabbatar da cewa akwai barazanar kai hare-haren, kamar yadda ya ke yawo a wata sanarwa da aka ce ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta bukaci mazauna Kano su yi taka tsan-tsan da guje wa wuraren da ke da cunkoso har sai an bayar da sanarwa ta gaba.
Kano: Yan sanda sun dauki matakan tsaro
Daily Post ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu daga harin da ake fargabar kai wa jihar.
A cikin wata sanarwa da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce:
“Wani rukunin ƙwararru daga sashen Rundunar Kula da Abubuwa Masu Fashewa, Harhada Sinadarai, Hanyoyin Kariya daga Nukiliya sun tashi tsaye don kare muhimmam wurare a Kano."
Za a iya tuntubar sashen ta lambobin: 08169884988 ko 07067157218 domin bayar da rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi.”

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
Rundunar yan sanda ta nemi hadin kai
Rundunar ‘yan sanda ta yi kira ga jama’a da su bayar da gudunmawarsu wajen tabbatar da tsaro ta hanyar bayar da bayanai da zarar sun ga abin da ba su amince da shi ba.
A cikin sanarwar, ta ce:
“Muna roƙon mazauna Kano su rika bayar da rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi ga mafi kusa da caji ofis, ko ta hanyar kira ga Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta lambobin gaggawa: 08032419754, 08123821575, 09029292926.”
“Taka tsan-tsan da haɗin kan jama’a suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsaron jama’a.”
"Za mu kare rayukan jama'a" - 'Yan sanda
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya jaddada aniyarsu ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar tare da tabbatar da zaman lafiya da doka a Kano.
A cikin sanarwar, rundunar ta gode wa al’ummar Kano bisa goyon bayansu tare da yin kira ga jama'a da su kwana da shirin barazanar hari.
'Yan sandan Kano sun kama 'yan fashi
A baya, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke wasu 'yan fashi da makami da ake zargi sun addabi mazauna birnin Kano da kewaye.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Kiyawa ya bayyana cewa wadanda aka kama sun amsa abin da ake zarginsu da shi, kuma sun sanar da rundunar muhimman bayanai a kan ayyukansu.
Asali: Legit.ng