Asiri Ya Tonu: Matasa Sun Yi Tara Tara, Sun Kama Malamai 2 da Wasu Abubuwan Ban Mamaki
- Matasa sun cafke wasu malaman coci a jihar Ribas bisa zarginsu da aikata wasu baƙin abubuwa, an gano kayayyakin ban mamaki a cocinsu
- Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa a binciken farko, ta gano alburushi mai rai, takobi da wasu akwatuna na itace
- Ɗaya daga cikin limaman cocin da suka shiga hannu, ya ce ya jima yana taimakon al'umma a yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Matasa sun ritsa wasu limamai biyu, sun kama su a jihar Ribas saboda gano alburushi da kayayyaki a majami'un da suke wa'azi.
Waɗanda ake zargin, Fasto Umoren Bassey da Fasto Elijah Aniete, sun shiga hannu ne ranar 20 ga Janairu, 2025, a kauyen Rumunduru da ke karamar hukumar Obio/Akpor.

Asali: Twitter
Bayan kama su, matasan ba su yi wata-wata ba suka miƙa su ga rundunar ƴan sanda, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa malaman cocin ba su wuce shekaru 60 da 51 ba a duniya kuma dukkansu ƴan asalin jihar Akwa Ibom ne.
Yan sanda sun tabbatar da cafke malamai 2
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta gabatar da wadanda ake zargin a hedkwatar ‘yan sanda da ke Fatakwal ranar Alhamis.
Ta bayyana cewa a binciken farko an gano abubuwa masu ban mamaki a cikin cocin da fastocin ke jagoranta.
Abubuwan da aka gano sun hada da harsashi mai rai, takobi, akwatuna biyu na itace, fasfon sufurin ruwa na jabu, hotuna da fasfon dubban mutane.
Abubuwan da aka gano a cocin limaman
Sauran abubuwan da aka gano a cocin sun hada da kwalabe dauke da sindarin da ba sani ba, takalman yara, akwatunan bokanci, kwakwa, littattafan Biyibul, kayan ‘yan sanda, da sauran kayan tsafi daban-daban.
Sai dai, babu maciji ko babban akwatin gawa kamar yadda rahotannin farko suka yi ikirari.
Kakakin ƴan sandan ta ce cocin Fasto Bassey mai suna God Deliverance Apostolic Church da ta Fasto Aniete mai suna Power House of Glory International Church suna kan titin Eneka a Rumunduru a karamar hukumar Obio-Akpor.
Fasto ya faɗi dalilin tara kayan a coci
Da yake jawabi, ɗaya daga cikin malaman cocin da aka cafke, Fasto Bassey ya ce yana amfani da kayan tsafi wajen yin addu’a kamar yadda Allah ya umarce shi.
Sai dai ya yi zargin cewa al’ummar yankin ne suka ƙulla masa makirci suka sanya wasu daga cikin kayan da aka gano a cocinsa sannan suka bincike gidansa ba tare da izini ba.
“Na dade ina warkar da mutane daga rashin lafiya kuma ina taimakon al’umma. Na yi shekaru 17 ina zama a wurin. Wasu daga cikin hotunan da kuka gani na da ne.
"Ina amfani da karamin akwatin gawa ko man al’ajabi wajen yi wa masu tabin hankali addu’a, duk mahaukacin da aka kawo mani yana samun nutsuwa cikin watanni uku, ina haka ne don taimakon mutane."
Wasu ƴan fashi sun shiga hannu
Kun ji cewa yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifin fashi da makami a jihar Kano.
Ƴan sanda sun gano kayayyaki a hannun ƴan fashin wada suka haɗa da wuƙaƙe da wayar salula, za a gurfanar da su a kotu bayan gama bincike.
Asali: Legit.ng