‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 9, Sun Sace Tsohon Daraktan CBN da Wasu 34 a Jihar Arewa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 9, Sun Sace Tsohon Daraktan CBN da Wasu 34 a Jihar Arewa

  • Tsagerun 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai kazamamin hari jihar Kaduna da Gwamna Uba Sani ke jagoranta
  • An rahoto cewa 'yan bindigar da ba'a san ko su wanene ba sun kashe mutum tara sannan suka yi garkuwa da wasu 35 ciki harda tsohon daraktan CBN
  • A halin da ake ciki, Gwamna Uba Sani ya ziyarci garuruwan da abun ya shafa sannan ya yi kira ga rundunar soji da ta gaggauta daukar mataki da magance matsalar tsaron jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa 'yan bindiga sun kashe mutum tara a garin Kwasam, karamar hukumar Kauru da garin Gwada a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mutum 35, ciki harda wani daraktan Babban Bankin Najeriya (CBN) mai ritaya, kaninsa da matar kaninsa.

Uba Sani ya bukaci sojoji da su karfafa ayyukansu a Kaduna
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 9, Sun Sace Tsohon Daraktan CBN da Wasu 34 a Jihar Arewa Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Yadda 'yan bindiga suka farmaki garuruwan Kaduna

A cewar majiyoyi, 'yan bindigar sun kuma jikkata mutum tara a hare-haren da suka kai kananan hukumomin biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, kungiyar mutanen Kudancin Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, 17 ga watan Fabrairu.

Wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta hannun kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Samuel Aruwan, ta kuma tabbatar da harin amma ta yi gum kan wadanda aka kashe da sacewa a karamar hukumar Kauru a Kudancin Kaduna.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigar sun aiwatar da harin kan garuruwan a yammacin ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Jaridar Leadership ta rahoto cewa 'yan bindigar sun kai mamaya daya daga cikin garuruwan, inda suka dauki mutane biyu da bindiga, suka jagorance su zuwa gidan tsohon ma'aikacin na CBN sannan suka sace shi.

An bayyana sunan tsohon ma'akacin na CBN a matsayin Zakariya Markus.

"Yan bindiga sun je gidan iyalinsa, suka sace kaninsa da matar kanin. Mazauna sun gaggauta fitowa a kokarinsu na ceto mutanen ammam 'yan bindigar suka yi ta harbi."

Uba Sani ya yi martani yayin da 'yan bindiga suka farmaki Igabi da Kauru

Da yake martani, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya roki jami'an sojoji da su kaddamar da zazzafan hare-hare kan 'yan bindiga a fadin jihar bayan wadannan hare-hare.

Gwamnan ya mika ta'aziyyarsa ga 'yan uwan wadanda suka rasa masoyansu a kananan hukumomin Igabi da Kauru.

'Yan sanda sun kama masu satar yara

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutum 10 bisa zargin satar yara da sayar da su.

Shehu Nadada, kwamishinan ƴan sandan jihar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke birnin Lafia a ranar Juma’a, cewar rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel