Ana Zargin Turji Ya Tsere Mahaifar Matawalle bayan Hare Haren Sojoji, Ya Sake Shiri
- Ana zargin cewa shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, yana cikin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara yayin da sojoji suka kara matsa masa
- Rahotanni sun ce an ga mabiyan Turji suna hijira a kan babura, dauke da raunana, zuwa wuraren Garsa/Kadanya a ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2025
- An yi zargin cewa Turji yana boye tare da wasu mabiyansa a Garsa/Kadanya, tare da goyon bayan tsohon abokin gaba, Jummo Smally
- Hakan bai rasa nasaba da irin matsin lamba daga rundunar sojojin Nigeriya a yan kwanakin nan da ke neman cin masa ta kowace hanya a Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Maradun, Zamfara - Yayin da sojoji ke kara matsin lamba kan shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, dan ta'addan ya sauya taku da kuma shirya gujewa dakarun.
Ana zargin Bello Turji yana cikin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara yankin da karamin Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya fito.

Asali: Facebook
Wasu manyan yan bindiga sun mika wuya
Wannan zargi ya fito ne daga shafin masanin tsaro, Zagazola Makama, a ranar Litinin 21 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da aka bayyana cewa wasu manyan shugabannin 'yan bindiga biyu, Abu Radde da Umar Black, sun mika makamansu a Katsina.
Yan ta'addan sun mika wuya ne sakamakon hare-haren dakarun soji na Operation Hadarin Daji da Operation Forest Sanity.
Shugabannin biyu, da suka ƙware wurin kai hare-haren garkuwa da satar shanu a Batsari da Safana, sun mika makamansu bayan hare-haren sama da na kasa sun hana su sake motsi.
Bello Turji ya rasa madafa bayan harin sojoji
Har ila yau, an tabbatar da cewa hatsabiban yan ta'addan sun saki wadanda suka yi garkuwa da su a lokuta da dama.

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin
The Guardian ta ce an samu bayanai da ke nuni da cewa Bello Turji yana Maradun domin ci gaba da ayyukan ta'addanci.
Wasu shaidan gani da ido sun ce mabiyan Turji, dauke da raunana, sun yi tattaki a kan babura daga Garsa/Kadanya zuwa Bayanruwa.
Majiyoyin sun ce maharan sun bi hanya daga Galadi, Damaga, Rudunu, zuwa Danbenchi.
Wasu kuma sun ce sun gan su a Rudunu, Bankamawa, da Farfaru a yankin Faru, ana zargin Bello Turji yana tare da dan bindiga, Jummo Smally a Garsa/Kadanya.
Wasu na ganin hakan ya nuna kashin rikakken dan ta'addan ya kusa bushewa duba da yanayin da ya shiga a yan kwanakin nan.
Bello Turji ya shirya kalubalantar sojoji
A baya, kun ji cewa awanni da kashe dansa, Bello Turji ya kafa sabon sansani a dajin Dutsi da Yan Buki bayan tafka mummunar asara a hare-haren sojoji.
Rahoto ya bayyana cewa Bello Turji ya mayar da sabon sansanin matsayin matattarar 'yan ta'adda da kula da wadanda aka raunata duk da barazanar sojoji da yake fuskanta.
Rundunar sojoji na ci gaba da samun nasarorin murkushe 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma a karkashin Operation Fansan Yanma da kuma hadin kan wasu al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng