Bello Turji Ya Komawa Malaman Tsubbu yayin da Ya Kusa Shiga Hannun Sojoji

Bello Turji Ya Komawa Malaman Tsubbu yayin da Ya Kusa Shiga Hannun Sojoji

  • Alamu sun nuna cewa ta'addancin Bello Turji a Zamfara, Sokoto da sauran jihoho masu makwabtaka da su ya kusa zuwa ƙarshe
  • Tantirin dan bindigan ya fara shiga ruɗani kan shirin da dakarun sojoji suke yi na ganin cewa ya shiga hannu domin ya girbi abin da ya shuka
  • Turji ya tattaro malaman tsubbu domin su yi masa addu'a ya samu kariya daga shirin da sojojin runduar Operation Fansan Yamma suke na cafke shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, ya fara neman hanyoyin da zai kaucewa kamun da dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma suke son yi masa.

Bello Turji a ƙoƙarin kaucewa faɗawa hannun jami'an tsaron, ya shirya tara malaman tsubbu da ke yi masa addu’a don kare shi daga farmakin sojoji.

Kara karanta wannan

Malami ya faɗi jihohi 8 da ƴan bindiga ke shirin kai hari, ya ce rayuwar sarki na cikin haɗari

Bello Turji ya tara malaman tsubbu
Bello Turji na tsoron kamun dakarun sojoji Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bello Turji ya tattara malaman tsubbu

Majiyoyi sun bayyana cewa ta’addancin Bello Turji ya jima yana samun goyon bayan malaman tsubbu waɗanda ke yin addu’o’i da ba da shawarwari kafin ya tura mutanensa zuwa wani farmaki.

Ana ganin cewa waɗannan malamai, da ake zargin sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar da Maiduguri, suna ɗora shi a kan hanya kan lokacin kai hari da irin hare-haren da ya kamata ya kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Bello Turji na neman taimakon ƴan tsubbu

“Ya zama al’ada ga Bello Turji ya tuntuɓi waɗannan malaman tsubbu kafin ya kai wani hari."
"Su ne ke ba shi umarni kan irin harin da ya kamata a kai da lokacin da ya fi dacewa, tare da ba da shawarwari kan dabarun gujewa farmakin sojoji."

Kara karanta wannan

Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

- Wata majiyar tsaro

Yayin da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi don cafke Bello Turji, ana jin cewa ya koma ga waɗannan malaman ne domin samun kariya daga hare-haren sojoji suke kai wa a Zamfara, Sokoto, da sauran jihohin da ke makwabtaka.

Karanta wasu labaran kan Bello Turji

Bello Turji ya shiryawa sojoji mugunta

A wani labarin kuma, kun ji cewa tantirin shugaban ƴan bindiga Bello Turji, ya ba mayaƙansa sabon umarni kan dakarun sojojin Najeriya.

Bello Turji ya umarci mayaƙan nasa da su yi wa dakarun sojojin kwantan-ɓauna a yankin Issah na jihat Sokoto, yayin da suke ci gaba da matsa masa lamba.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta sake taso Bello Turji a gaba, ta fadi abin kunyar da ya yi

Unarnin na Bello Turji na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun taso shi a gaba inda suke kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa a maɓoyarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng