Ana cikin Firgici a Neja: Mutanen da Suka Mutu a Fashewar Tankar Mai Sun Haura 85

Ana cikin Firgici a Neja: Mutanen da Suka Mutu a Fashewar Tankar Mai Sun Haura 85

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta Niger ta ce an yi jana'izar mutum 86 daga cikin wadanda suka mutu a fashewar tankar mai
  • Masu aikin sa kai daga Gurara tare da wasu 'yan uwan wadanda abin ya shafa suka gudanar da jana'izar a cibiyar lafiya ta Dikko
  • Wasu daga cikin wadanda suka tsira daga gobarar sun fadi yadda suka rasa 'yan'uwansu yayin da aka kwantar da wasu 43 a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - An sanar da cewa an yi jana'izar mutum 86 daga cikin wadanda suka mutu a fashewar tankar man fetur a ranar Asabar a asibitin Dikko.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana cewa an yi jana'izar mutanen ne bisa haɗin gwiwa da jami'an karamar hukumar Gurara da masu aikin sa kai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Gwamnati ta yi magana yayin da aka binne gawar mutane 86 bayan fashewar tankar mai a Neja
Adadin wadanda suka mutu a fashewar tankar mai a Neja ya kai 86. Hoto: @UsmanBaba09
Asali: Twitter

An birne gawar mutane 86 a Neja

Daraktan hukumar, Abdullahi Baba-Arah, ya ce an yi jana'izar ne daga karfe 5:00 na yamma zuwa tsakiyar dare a cibiyar lafiya ta Dikko, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baba-Arah ya ce an birne yawancin wadanda suka rasu a cikin kabari daya, amma an dauke wasu gawarwaki biyar zuwa garuruwan su don birne su a can.

Shugaban hukumar ya ce an samu wani mutum daya da ya mutu a cikin cibiyar kiwon lafiyar, kuma an hada da shi a cikin wadanda aka yiwa jana'iza a ranar.

Yadda mutane suka mutu a fashewar tankar

An ce wata tankar mai ce ta kama da wuta bayan ta fadi, lamarin da ya jawo wutar ta cinye mutane da dama a garin Dikko, kan hanyar Neja zuwa Kaduna.

Shaidun gani da ido sun ce mazauna yankin sun fara dibar man fetur daga cikin tankar da ta fadi, inda fashewar tankar ya kashe mutane da dama.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Wutar ta laso har da wasu matafiya da ke wucewa ta kan hanyar, wanda ya jawo mutuwar wasu da jikkata wasu, da kuma lalata shagunnan 'yan kasuwar yankin.

Neja: 'Yan kasuwa sun rasa dukiyoyinsu

Mazauna yankin da wadanda suka tsira daga gobarar sun ba da labarin irin masifar da suka gani, da kuma yadda wutar ta kashe 'yan uwansu.

Wani daga cikin wadanda suka tsira, Mohammed Shehu, ya ce yana zaune a cikin shagonsa a geffen titi lokacin da wutar ta kama shagon.

Mohammed ya ce ya yi ta maza ya fita daga shagon domin tsira da rayuwarsa kuma yana ji yana gani wutar ta kone shagon.

Bashir Usman, wani mazaunin Dikko, ya ce ya rasa 'yan'uwansa uku, Musa, Ka'ab da Ibrahim da kuma shagunansa uku na miliyoyin Naira.

Neja: Yadda mutane suka rasa 'yan uwansu

Wani dan kasuwa, Abubakar Jibril, daga garin Maje, ya bayyana cewa ya rasa shaguna bakwai da kayayyaki na miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

Jibril ya ce ya rasa kayayyaki masu daraja na Naira miliyan 20, sannan 'yan kasuwar da ke makotaka da shi sun rasa shaguna sama da 10.

Adamu Ahmed, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa ya rasa 'yan'uwansa shida da abokansa a cikin wutar.

An ce akwai wani Yusuf Maidawa, wanda ya sauka garin daga Minna tare da matarsa Mariyama da dan'uwansa, wanda wutar ta halaka shi da dan uwan nasa.

Tinubu ya yi ta'aziyya ga mutanen Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kadu da samun labarin hatsarin da ya kashe mutane da dama a jihar Neja.

Shugaban kasar ya gargadi jama’a da su guji zuwa wurin da tankar mai ta fadi, domin kaucewa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.