Karfin Hali: Dan Ta'adda Ya Kai Ziyarar Jaje Gidan Mutanen da Ya Yi Garkuwa da Su
- Jami'an tsaro sun yi ram da wani da ake zargin da garkuwa da mutane a kauyen Sabon-Gari Mangu Matachibu a jihar Neja
- Rundunar ‘yan sandan Neja ta gano karbe makamai daga hannun Nasiru Isyaka, wanda ya amsa laifin garkuwa da mutane
- An kama wanda ake zargi ne bayan shi da tawagarsa sun yi garkuwa da wasu bayin Allah, tare da kashe mutum guda a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Wani da ake zargin dan ta’adda ne ya wuce gona da iri yayin da aka gano shi yayin ziyarar ta’aziyya a gidan daya daga cikin wadanda ya sace a Karamar Hukumar Kontagora, Jihar Neja.
Kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce wanda ake zargin, Nasiru Isyaka, da tawagarsa sun kutsa Sabon-Gari Mangu Matachibu, inda suka kashe mutum guda, sannan suka sace mutane biyu.

Asali: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa Isyaka ya tafi ziyarar ta’aziyya a gidajen wadanda aka sace, lokacin da wanda aka yi garkuwa da shi ya gane shi a matsayin guda daga cikin masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama dan ta’adda a Neja
Jaridar Pulse ta ruwaito cewa a lokacin da wanda aka yi garkuwa da shi ya ankare ne ya shaida wa mutanen da ke wajen, inda aka gaggauta daukar matakain da ya dace a hukumance.
A cikin wata sanarwa da Wasiu Abiodun ya fitar, ya ce;
“Ranar 17 ga Janairu, 2025, a kimanin karfe 10 na safe, jami’an ‘yan sanda na ‘A’ Div Kontangora sun kama Nasiru Isyaka na Sabon-Gari Mangu Matachibu, a Karamar Hukumar Kontangora.”
“An kama shi ne saboda garkuwa da mutane da aka yi a ranar 29 ga Disamba, 2024, a wannan kauye, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari, suka kashe mutum guda sannan suka sace mutane biyu, sai dai daga bisani an ceto su ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
“A cikin binciken farko, an kama shi lokacin da ya tafi ziyarar daya daga cikin wadanda aka ceci a gidansa, inda aka gane shi a matsayin daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.”
An kama dan ta’adda da makamai
Rundunar ‘yan sandan Neja ta bayyana cewa an samu makamai daga hannun mutumin da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar.
Rundunar ta ce:
“An samu bindiga kirar gida daga dan ta’addan, kuma ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.”
“An tura shi zuwa hedkwatar ‘yan sanda ta Minna don ci gaba da bincike da gurfanar da shi a kotu.
“Ana ci gaba da kokarin kamo sauran mambobin dabarsa.”
Ganduje ya ba da dabarar kakkabe 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sojojin Najeriya su inganta salon aikinsu ta hanyar mamaye dazuzzuka domin kakkabe ‘yan ta’adda.
A cewarsa, amfani da dabarun tsaro na kai hari maimakon na kare kai zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a kasar cikin gaggawa, ciki har da kai hare-hare cikin dazuzzukan kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng