Sako Mai Taba Zuciya da Shugaba Tinubu Ya Turawa Iyalan Wadanda Suka Mutu a Gobarar Neja

Sako Mai Taba Zuciya da Shugaba Tinubu Ya Turawa Iyalan Wadanda Suka Mutu a Gobarar Neja

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kadu da samun labarin hatsarin da ya kashe mutane da dama a jihar Neja
  • Shugaban ya gargadi jama’a da su gujewa zuwa wurin da tankar mai ta fadi don gudun asarar rayuka da dukiyoyi
  • A kan samu hadurra da ke kai wa ga mutuwar mutane da dama, hakan ya zama ruwan dare a kasar mai tarin jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhini kan mummunar gobarar tankar mai da ta hallaka fiye da mutane 80, tare da jikkata da dama a Dikko Junction, karamar hukumar Gurara, Jihar Neja.

Wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar Asabar, inda ya bar baya da jimami ga iyalan wadanda suka rasu da kuma al’ummar Jihar Neja baki daya.

Tinubu ya mika sakon ta'aziyya
Sakon da Tinubu ya turawa 'yan Neja | Hoto: A. Majeed/@officialABAT
Asali: UGC

Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari mai tayar da hankali, tare da mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar Neja da daukacin al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

Ana maganar 'Qur'anic Festival', gwamnati ta fito da shiri ga almajiran Najeriya

Sakon Tinubu ga ahalin wadanda suka jikkata

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a ranar 19 ga watan Janairu, 2025 ta shafinsa na X (Twitter).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sakonsa, shugaban kasa ya jaddada cewa wannan lamari abin takaici ne saboda ana iya kauce masa.

Yawancin wadanda suka rasa rayukansu, a cewarsa, sun kasance ne suna kokarin debo man fetur daga tankar da ta yi hatsari.

Mafitar da shugaba Tinubu ya kawo

Domin saukaka wahalar da wannan ibtila’in ya jawo, Shugaba Tinubu ya umarci a samar da cikakken kulawar lafiya ga wadanda suka jikkata a wannan gobara.

Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin tsaro da na kiyaye hadurra su dauki matakan gaggawa don hana faruwar irin wannan al’amari nan gaba.

A yayin gargadi, Shugaban kasa ya shawarci jama’a da su guji kusantar wuraren da hatsari ya faru, musamman idan ya shafi motoci dauke da mai.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Za a fara wayar da kan 'yan Najeriya

Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) da ta fara gangamin fadakarwa a duk fadin kasar.

Wannan wayar da kai zai mayar da hankali ne wajen ilmantar da jama’a kan hatsarin debo mai daga motar da ta yi hatsari, tare da illar hakan ga muhalli da lafiyar jama’a.

Shugaban kasa ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya ba iyalansu hakurin jure wannan rashi, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Daga karshe, jama’a ana bukatar su kasance masu lura da tsaro da kauce wa duk wani abu da zai iya jefa su cikin hadari, domin kare rayuka da dukiyoyin su.

Yadda mutane suka mutu a Neja

Idan baku manta ba, mun ruwaito muku yadda tankar mai ta tashi da wuta bayan faduwa a jihar Neja, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da yawa.

Kara karanta wannan

Matasa sun sake zuwa diban fetur da tanka ta fadi, yan kasuwa sun tsere

Rahotanni sun bayyana cewa, mutane sun taru don debo man da ya zube a motar, wannan ya kai ga suka kone.

Irin wannan ya sha faruwa a Nejeriya, wanda a yanzu ya zama babban kalubale ga mazauna yankunan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.