'Yan Najeriya ba Su Jin Gargadi Har Yanzu': Buhari Ya Koka kan Iftila'in da Ya Faru a Niger
- Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan iftila'in fashewar tankar mai da ya faru a jihar Niger
- Buhari ya nuna takaicin rashin jin gargadin hukumomi da mutane ke yi game da haɗarin ɗaukar man fetur daga tankar da ta fashe
- Tsohon shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da Gwamnatin Neja bisa tashin hankalin fashewar tankar mai a kwanar Dikko
- Wannan na zuwa ne bayan hukumar ba da agaji ta NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 86 da kuma wasu 55 da suka samu raunuka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a jihar Niger.
Buhari ya bayyana takaicinsa kan yadda 'yan Najeriya ba su jin gargadin hukumomi game da tankokin man fetur da ke fashewa.

Asali: Facebook
An kara samun gawarwaki a jihar Niger
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a harkar watsa labarai, Garba Shehu, ya fitar a shafin X a yau Lahadi 19 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan fashewar wata tankar mai da ta kashe mutane da dama a Jihar Neja a ranar Asabar, 18 ga Janairu, 2025.
Yawan mutane da suka mutu a gobara daga fashewar tankar fetur a Dikko da ke jihar Niger sai karuwa yake yi.
Aƙalla a yanzu mutane da suka mutu sun kai 86, yayin da 55 suka jikkata, an kuma yi jana’izar gama-gari.
Gwamnan Niger, Mohammed Umar Bago, ya hana ababen hawa daga hanyar Maje amfani da gadar Dikko, yana mai nuna takaici.
Buhari ya tura sakon ta'azziya ga yan Niger
A martaninsa kan lamarin, Buhari ya jajanta wa iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Jihar Neja.
Dattijon ya ce abin takaici ne kwarai yadda aka rasa rayukan al'umma duk da dai akwai sakacin mutane kan haka.
“Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa game da asarar rayuka sakamakon gobarar da ta biyo bayan fashewar wata tankar mai."
"Lamarin ya faru ne a kwanar Dikko da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a Ƙaramar Hukumar Gurara da ke jihar Niger."
- Muhammadu Buhari
Buhari ya fusata da rashin jin gargadi
Buhari bayyana takaicinsa kan yadda mutanen ke ci gaba da tattara mai daga tankokin da suka fashe duk da gargadin hukumomi da kuma asarar rayuka da ake yi sakamakon haka.
Yayin da yake jajantawa Gwamnatin Jihar Neja da mutanen jihar, tsohon shugaban ya yi fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
Gwamna Bago ya shawarci gwamnonin Arewa
Kun ji cewa Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa su yi amfani da Hausa a matsayin harshen koyarwa a makarantu.
A cewar Gwamna Bago, Turanci ya kamata ya zama darasi ne kawai a makarantun firamare da sakandare a Arewa, ba harshen koyarwa ba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa.
Asali: Legit.ng