Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin da zai sa a Sauke Farashin Fetur

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin da zai sa a Sauke Farashin Fetur

  • Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa farashin man fetur yanzu ya dogara ne da yadda kasuwannin duniya ke tafiya
  • Heineken Lokpobiri ya ce an kawo karshen tallafin man fetur gaba ɗaya, kuma gwamnati ta mayar da hankali kan inganci da wadatar man fetur
  • Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa haɗin gwiwa da matatar Dangote ya rage farashin mai a kasuwannin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya ce gwamnati ba ta da hannu wajen tsayar da farashin fetur tun bayan da aka kammala cire tallafin man fetur.

A wani taron masu ruwa da tsaki a bangaren albarkatun man fetur, ministan ya bayyana cewa farashin danyen mai a kasuwannin duniya ke yin tasiri kai tsaye ga farashin mai a cikin gida.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Man fetur
Gwamnati ta cire hannu kan farashin mai. Hoto: Bayo Onanuga|Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministan ya yi bayani ne yayin da ake fargabar karin kudin man fetur bayan farashin gangar danyen mai ya kai Dala 80.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta cire hannu kan farashin mai

Lokpobiri ya ce bayan an kawo karshen tallafin man fetur, yanzu gwamnati ta mayar da hankali kan tabbatar ingancin mai.

Ministan ya bayyana cewa za a cigaba da sayar da man fetur ne a farashin da kasuwa ta zo da shi ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

A cewar ministan;

“Manufar zare hannun gwamnati a kan fetur ita ce farashi ya dogara da yadda kasuwa ta kasance.
"A da, kullum kuna jin labaran matsaloli kan tallafin man fetur. Yanzu, babu wani labarin tallafi domin an kawar da shi gaba ɗaya.”

Me zai saka farashin mai sauka?

Heineken Lokpobiri ya kara da cewa farashin danyen mai a kasuwar duniya ne zai iya kawo saukar farashi ko tashinsa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

“Idan farashin danyen mai ya hau, farashin fetur zai hau, idan kuma ya sauka, farashin fetur zai sauka.
A lokacin Kirsimeti, na zagaya gidajen mai daban-daban a Bayelsa, wasu suna siyar da N1,020, wasu N999, wasu kuma N1,015.”

- Heineken Lokpobiri

Ministan ya ce gwamnati ta fi damuwa kan tabbatar da cewa masu siyan mai ba sa asara a cikin adadin man da ake siyar musu a gidajen mai.

Vanguard ta wallafa cewa ministan ya ce idan mutum ya saye lita 10 a gidan mai, ya kamata ya samu lita 10 cif-cif ba tare da kari ko ragi ba.

Haɗin gwiwa da Dangote ya saukaka farashi

Shugaban kungiyar (IPMAN), Abubakar Maigandi ya bayyana cewa haɗin gwiwar da aka cimma tsakanin kungiyar da matatar Dangote ya taimaka wajen rage farashin mai a kasuwa.

A cewar Abubakar Maigandi;

“Mun fara lodin mai daga matatar Dangote tare da MRS tun daga ƙarshen shekarar da ta gabata, wanda ya sa muka rage farashin mai fiye da sauran masu siyarwa.”

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya suka fada bayan Buhari ya yi kyautar daloli

Ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar ta tabbatar da cewa akwai daidaitaccen farashi a dukkan wuraren siyar da mai a ƙasar nan.

Rage dogayen layuka a gidajen mai

Heineken Lokpobiri ya ce tsarin gasa a kasuwa yana bai wa jama’a damar zaɓi, wanda hakan ya rage jerin layuka a gidajen mai.

A cewar Lokpobiri lokacin da aka samu gasa, mutane na da damar zaɓin gidan man da za su saye fetur a fadin Najeriya.

An samu man fetur a Rwanda

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Rwanda ta sanar da cewa ta samu nasarar hako danyen man fetur a karon farko.

Bayan samun nasarar, kasar Rwanda ta bayyana cewa za ta cigaba da kokarin gano wasu rijiyoyin man fetur a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng