An Kaddamar da Rabon Tallafin Kudi ta Banki, Gwamna Zai Raba Naira Biliyan 4.9
- Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon tallafi NG-CARES domin tallafawa mutane marasa ƙarfi a fadin jihar
- Tallafin ya shafi mutane 44,000 daga kananan hukumomi 14, inda gwamnati ta ware Naira biliyan 4.964 domin rabawa
- Shirin ya haɗa da nau’o’in tallafi guda huɗu, wanda ya haɗa da kuɗin tallafi na wata-wata da taimako ga masu ƙananan sana’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - A wani yunƙuri na tallafawa marasa ƙarfi, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon tallafin NG-CARES ga mutane 44,000 a jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kaddamar da rabon tallafin ne a dakin taron Garba Nadama a birnin Gusau na jihar Zamfara.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya wallafa yadda shirin ya gudana a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a raba Naira biliyan 4.964 ga marasa karfi
Gwamna Lawal ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 4.964 domin rabawa ga marasa ƙarfi a jihar Zamfara.
Rahoton TVC ya nuna cewa shirin ya ƙunshi tallafin wata-wata na N20,000 ga marasa karfi na shekara guda, inda kaso 60% za su kasance mata, kashi 40% kuma maza.
Tallafin marasa lafiya da kananan sana’o’i
A cikin tsarin tallafin kudin, an ware N10,000 ga tsofaffi, masu bukata ta musamman, da masu fama da tsananin rashin lafiya na tsawon shekara guda.
Haka kuma, za a bai wa masu ƙananan sana’o’i N150,000 domin farfado da sana’o’in su da haɓaka tattalin arzikin al’umma.
Tallafin kudi ga mata da 'yan agaji
Gwamnan ya bayyana cewa an kuma ware N50,000 domin tallafawa mata, 'yan agaji, malaman makarantar allo da Islamiya domin fara sana'o'i.
Dauda Lawal ya bayyana cewa an tsara tallafin ne domin inganta sana’o’in gida da ƙarfafa tattalin arzikin a jihar.
Gwamnan Neja zai tallafawa dalibai mata
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Neja ta fara shirin samar da kwamfutoci masu tarin yawa ga ɗaliban makarantun gwamnati.
Legit ta ruwaito cewa gwamna Umaru Bago ya fara shirin daukar nauyin karatun mata 1,000 kowace shekara domin karatu a fannin kiwon lafiya.
Asali: Legit.ng