An Shiga Jimami Yayin da Babbar Mota Ta Yi Ajalin Yarinya Mai Shekara 5 a Lagos

An Shiga Jimami Yayin da Babbar Mota Ta Yi Ajalin Yarinya Mai Shekara 5 a Lagos

  • Wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Bosede ta gamu da ajalinta a wani hatsari a hanyar Iganmu zuwa Apapa a jihar Legas
  • Wani direban babbar mota ya murkushe yarinyar har lahira yayin da suke tsallakawa kan babbar hanyar tare da mahaifiyarta
  • Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce ‘yan sanda na kan farautar direban da ya gudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iganmu, Lagos state - Wani direban babbar mota ya murkushe wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Bosede har lahira a hanyar Iganmu zuwa Apapa a jihar Legas.

Mummunan lamarin ya faru ne a lokacin da yarinyar ke ketara babban titin Iganmu karkashin gada tare da mahaifiyarta, a ranar Asabar, 11 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Dalibai 14 cikin 24 da aka sace a jami'ar Kogi sun kubuta, 'yan sanda sun yi bayani

Mota ta murkushe yarinyar 'yar shekara 5 a Lagos
Babbar mota ta bi ta kan yarinya 'yar shekara 5 a Lagos, ta mutu nan take. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

Mota ta murkushe 'yar shekara 5

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an kai rahoton afkuwar hatsarin ga ofishin ‘yan sanda na Iponri ranar Asabar da misalin karfe 11:30 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, kakakin rundunar 'yan sandan ya ce yarinyar da mahaifiyarta na tsallakawa kan titin ne sai motar ta murkushe ta har lahira.

Ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda na sashen kula da zirga-zirgar ababen hawa ne suka kwashe gawar daga inda hadarin ya faru.

Hundeyin ya ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike domin cafke direban motar wanda ya gudu, inji rahoton Peoples Gazette.

Mota ta murkushe masu sharar titi

A baya ma irin wannan ta faru inda wata mota ta murkushe wasu mata guda biyu har lahira a kan hanyar Oshodi zuwa Gbagada a jihar Lagos.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 4 da jami’an FRSC a wani kazamin hari a Enugu

Shaidun gani da ido sun bayyana wa manema labarai cewa wadanda suka mutun 'yan gida daya ne da suke aikin share tituna a birnin.

Babbar mota ta yi ajalin basarake

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa wata babbar mota babbar mota ta murkushe wani mai rike da sarautar gargajiya a karamar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun har lahira.

Marigayin mai suna Oba Abraham Bankole ya rasa ransa ne bayan motar ta bi ta kanshi a kan hanyar Ota-Idiroko a kokarinsa na saukowa daga adaidaita sahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel