Borno: Gwamna Zulum Ya Tafka Babban Rashi Yayin da Hadiminsa Ya Rasu

Borno: Gwamna Zulum Ya Tafka Babban Rashi Yayin da Hadiminsa Ya Rasu

  • Hadimin gwamnan jihar Borno a ɓangaren harkokin al'umma, Cif Kester Ogualili ya riga mu gidan gaskiya a yau Asabar
  • Hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Abdurrahman Ahmed Bundi shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 4 ga watan Mayu
  • Gwamna Zulum ya mika ta'aziyya zuwa ga iyalan marigayin inda ya musu addu'ar jure wannan babban rashi da aka yi a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya tafka babban rashi a gwamnatinsa.

Zulum ya rasa mai bashi shawara kan harkokin al'umma, Cif Kester Ogualili a yau Asabar 3 ga watan Mayu.

Hadimin Gwamna Zulum ya rasu bayan fama da jinya
Gwamna Babagana Zulum ya rasa hadiminsa, Cif Kester Ogualili. Hoto: Abdurrahman Ahmed Bundi.
Asali: Facebook

Yadda Ogualili ya shafe rasuwarsa a Borno

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa tsohon shugaban sojojin Najeriya a shirgegen mukami a jiharsa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Abdurrahman Ahmed Bundi ya fitar a shanfinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bundi ya tabbatar da cewa Ogualili ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da ke jihar bayan fama da jinya.

Marigayin ɗan asalin jihar Anambra ne wanda ya fito daga karamar hukumar Dunukofia amma ya shafe tsawon rasuwarsa a jihar Borno.

"Ina bakin cikin sanar da ku cewa Hon. Kester Ogualili ya rasu, marigayin ya yi wa jihar Borno aiki tukuru wanda ya kasance mai son zaman lafiya kuma jakadan al'ummar Igbo."
"Zamu ci gaba da tuna shi a matsayin wanda ya kawo hadin kai tsakanin al'ummar da ke rayuwa a jihar Borno."

- Ahmed Bundi

Zulum ya jajantawa iyalan marigayin a Borno

Gwamnan ya jajanta iyalan marigayin inda ya yi musu addu'ar hakurin jure wanna babban rashi da suka yi.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta koka kan yadda Borno ke biyan 'yan fansho N4,000 a wata

Ogualili ya riƙe muƙamin hadimin a bangaren harkokin al'umma a mulkin tsohon gwamnan jihar, Kashim Shettima daga 2011 zuwa 2019.

Zulum ya sake nada shi a muƙamin daga 2019 zuwa 2023 kafin daga bisani ya sake nada shi a 2024.

Ɗan marigayi Shehun Borno ya rasu

Kun ji cewa babban ɗan marigayi Shehun Borno, Alhaji Mustapha Umar El-Kanemi ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin wanda ɗa ne ga tsohon Shehun Borno wanda ya rasu ya kwanta dama a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel