Rikicin Rivers: Fubara Ya Ga Ta Kansa Yayin da Kwamishinoni 2 Suka Ajiye Aiki

Rikicin Rivers: Fubara Ya Ga Ta Kansa Yayin da Kwamishinoni 2 Suka Ajiye Aiki

  • An samu karin kwamishinoni biyu da suka yi murabus daga gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Rivers
  • A yau Laraba, kwamishinan ilimi na jihar Rivers, Prince Chinedu Mmon da takwaransa na ma'aikatar gidaje, Gift Worlu suka ajiye aiki
  • An ruwaito cewa, Prince Mmon da Hon. Worlu suna biyayya ne ga ministan Abuja, Nyesom Wike, da aka ba kwamishina bayan sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Kwamishinan ilimi na jihar Rivers, Prince Chinedu Mmon da takwaransa na ma'aikatar gidaje, Gift Worlu sun yi murabus daga gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara.

Kwamishinoni 2 sun yi murabus a jihar Rivers
Rivers: Kwamishinan ilimi da na ma'aikatar gidaje sun yi murabus daga gwamnatin Fubara. Hoto: Raphael B. Miitee, Journalist KC
Asali: Facebook

Wasu karin kwamishinonin Rivers sun ajiye aiki

An ce Mmon da Worlu suna biyayya ne ga ministan Abuja, Nyesom Wike, kuma a yanzu su ne kwamishinoni na hudu da aka sake nadawa da suka mika takardar murabus din.

Kara karanta wannan

Kwamishina na 4 ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tura wasiƙa ga Gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Prince Chinedu Mmon ya aika wa gwamnan da wasikar murabus dinsa ne a ranar 15 ga watan Mayu ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo, The Punch ta ruwaito.

Tsohon Kwamishinan Ilimi, ya ce ya yi murabus ne saboda wajen aikinsa na yanzu ya zama tamkar guba a gare shi.

Hon. Mmon ya roki magoya bayansa da su karbi wannan matakin da ya dauka na yin murabus daga gwamnatin Fubara da hannu biyu-biyu.

Rivers: Kwamishinoni 2 suka yi murabus

Talabijin na Channels ya ruwaito, tsohon kwamishinan gidaje, wanda ya ajiye aiki jim kadan bayan Mmon, ya ce matakan da Fubara ya ke dauka sun wuce gona da iri.

A baya mun ruwaito cewa tsohon Atoni-Janar kuma kwamishinan shari'a, Farfesa Zacchaeus Adangor ya fara mika takardar ajiye aiki.

Bayan tafiyar Farfesa Zacchaeus, tsohon kwamishinan kudi, Isaac Kamalu, shi ma ya aika wa Gwamna Fubara da takardar ajiye aiki.

Kara karanta wannan

"Tsohon gwamna Nyesom Wike ya tarawa Ribas Bashi," Simi Fubara ya fasa kwai

EFCC na neman Gwamna Fubara?

A wani rahoton bincike da muka fitar, mun fayyace gaskiya kan wani labari da ake yadawa a intanet da ke nuna cewa hukumar EFCC na neman gwamnan jihar Rivers ruwa a jallo.

Binciken da muka yi ya nuna cewa wannan labarin kanzon kurege ne, EFCC ba ta neman Gwamna Siminalayi Fubara, kuma hoton da aka yi amfani da shi tun na shekarar 2018 ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel