Yadda Ake Hada Kai da Jami’an tsaro da Jami’an Gwamnati, Ana Sace Man Najeriya

Yadda Ake Hada Kai da Jami’an tsaro da Jami’an Gwamnati, Ana Sace Man Najeriya

  • Bincike ya nuna akwai hannun jami’an tsaro da manyan gwamnati a satar man da ake yawan yi a yankin Neja-Delta
  • Tsageru su kan fasa bututun danyen mai, sai su saidawa manyan barayin da suke ciniki da kasashen waje a kan teku
  • Har yau Gwamnati ba ta kawo karshen barnar da ake yi ba, duk da Najeriya tana asarar Dalolin kudi kusan duk rana

Nigeria - Wadanda ake hada-kai da su wajen satar arzikin man Najeriya sun kunshi ‘yan siyasa, jami’an tsaro, ‘yan kasuwa, tsagerun Neja-Delta da hukuma.

Wani bincike da jaridar Vanguard ta gudanar a makon da ya gabata, ya fallasa yadda wadannan gungun mutane suke da hannu a badakalar satar danyen mai.

Tsagerun Neja-Delta suna sace danyen mai daga bututu a Neja-Delta, yayin da su ma’aikatan gwamnati suke agaza masu ta hanyar tunkudo danyen man.

Kara karanta wannan

Saurayi Da Budurwa da Suka Fara Soyayya A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu

Akwai kananan tsageru da ke satar danyen mai daga bututun Najeriya, sai su saidawa manyan barayi, wadannan manya na saida man ga kasashen waje.

Masu wannan danyen aiki sun hada-kai da jami’an tsaro wadanda suke nuna masu yadda za su dauki jirgin man da suka sata domin saidawa barayi a kan teku.

Rahoton yace duk jami’in tsaron da yake wannan danyen aiki, yana samun makudan kudi duk wata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamfanoni sun koka da masu aika-aika

Kamfanonin mai kamarsu Shell Petroleum Nigeria Limited, Chevron Nigeria Limited da NNPC sun dade suna kokawa da barnar da bata-gari suke yi a Najeriya.

Wani jami’in SPDC, Igo Weli ya nuna cewa babu shakka manya suna cikin barayin man domin talaka ba zai iya mallakar kayan aikin da ake amfani da su ba.

Jirgi
Jirgin ruwan A499 Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Shugaban bankin United Bank for Africa, Tony Elumelu ya taba cewa Najeriya tana asarar abin da ya kai 95% na arzikin man da da ake da shi ta dalilin barayi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yadda Tinubu da Gwamnonin PDP 4 Ke Shirya Yarjejeniyar Taimakon Juna

Su wanene ke wannan aiki?

Jaridar tace duk abin da ake yi, gwamnati ba ta taba kokari da kyau domin bankado wadanda suke satar dukiyar al’umma, suna saidawa kasashen ketare ba.

Ana zargin gwamnati ta san manyan barayin, amma na cigaba da zura masu ido, ana nunawa shugaban kasa cewa kananan tsageru suke tafka wannan sata.

A 2019 aka ji Gwamna Nyesom Wike yana fadawa Duniya jami’an sojoji suna da hannu a duk wajen satar danyen mai da bata-gari suke yi a jiharsa ta Ribas.

Wike ya zargi wani babban soja da ke Ribas da laifin taimakawa wadanda suke sace dukiyar kasa, yace da sojojinsa ake saida man da aka hako a Neja-Delta.

Tompolo ya samu kwangila

A lokacin da Najeriya take asarar tsadar da mai ya yi a kasuwa a Duniya, sai aka ji NNPC ya ba Government Ekpemupolo kwangilar da za su samu biliyoyi.

Kara karanta wannan

Yadda Rashin Tsaro Ya Jawo Aka Rufe Makarantu Fiye da 600 a Jihohin Najeriya

Kamfaninsu Government Ekpemupolo (Tompolo) aka ba kwangilar bada kariya ga bututun mai a Neje Delta, duk wata za su tashi da N48bn a duk shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel