Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Karin Haske Kan Rade Radin Kai Hari a Abuja

Rundunar ’Yan Sanda Ta Yi Karin Haske Kan Rade Radin Kai Hari a Abuja

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta magantu a kan wani faifayin bidiyo da ke yadawa da sunan an kai hari a Abuja
  • Shugaban rundunar kasar, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya karyata lamarin yau Alhamis, 25 ga watan Afrilun 2024
  • Ya kuma bayyana inda abin ya faru tare da lissafa irin matakan da hukumar za ta dauka a kan masu yada labarun karya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan wani faifayin bidiyo da ake yadawa da sunan an kai hari kan masu ababen hawa a Abuja.

Police IG
Shugaban yan sanda ya ce za a hukunta masu yada jita-jita. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Gaskiyar lamarin

Rundunar ta ce sakamakon binciken da jami'anta suka yi ya nuna faifayin bidiyon an yi shi ne a kasar Habasha.

Kara karanta wannan

Kano: An karrama yaro dan shekara 16 da kujerar hajji saboda Kur'ani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayanin da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa wani mutum ne ya tura bidiyon a shafinsa na X yana korafi a kan yawan kai hare-hare a Habasha.

Amma sai marasa kishin kasa suka sauya zancen da sunan a Abuja abin yake faruwa saboda su kawo firgici cikin al'umma.

Rundunar 'yan sanda ta dauki mataki

A cewar rundunar, saboda kaucewa faruwar haka a gaba, shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya bada umarnin yin cikakken bincike a kan wadanda suka kirkiro karyar.

Ya ce da zarar an gano su, hukumar za ta dauki matakin da dokar Najeriya ta tanada a kan masu aikata laifi irin nasu.

Shugaban 'yan sandan ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya a kan su rika taka tsantsan da tantance bayanai kafin aiki ko yada su.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya shawo kan matsalar da ta kawo dogon layi a gidajen mai

A karshe ya ce rundunar yan sanda za ta cigaba da sa ido a kan dukkan masu yada labaran karya da kuma daukan mataki a kan su.

An kama masu laifi a Sokoto

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutanen da ake zargi da tada tarzoma a kasuwar jihar Sokoto

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi fada tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a kasuwar, inda aka kashe mutane shida a rikicin

Asali: Legit.ng

Online view pixel