'Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 da Ake Zargi da Hannu Rikicin da Ya Barke a Kasuwar Sokoto

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 da Ake Zargi da Hannu Rikicin da Ya Barke a Kasuwar Sokoto

  • Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu mutanen da ake zargi da tada tarzoma a kasuwar jihar Sokoto a kwanan
  • An yi fada tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a wata kasuwar shanu, inda aka kashe mutane shida a rikicin
  • Jihar Sokoto na daya daga jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da rikicin ‘yan bindiga, musamman a shekarun baya

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Sokoto - Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a karamar hukumar Gada da ke jihar.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun halaka sojoji da dama a wani mummunan kwanton bauna

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ajihar, ASP Ahmed Rufa’i ne ya bayyana hakan yayin zantawa da jaridar Punch ta wayar tarho a ranar Lahadi.

'Yan sanda sun kama masu laifi a jihar Sokoto
AN kama wadanda ake zargi da tada zaune tsaye a Sokoto | Hoto: NPF
Asali: Facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kashe mutane shida a wata tarzomar da ta tashi tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a karamar hukumar Gada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin barkewar rikici a kasuwar Sokoto

Wata majiya ta ce, ‘yan banga a yankin, sun yi ramuwar gayya ce ta kashe shugabansu, wani da ake kira Alhaji Dahiru da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe.

Lamarin dai kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, ya fara ne a lokacin da wani shugaban ‘yan banga na kauyen Gidan Hashimu ya yi yunkurin cafke wani barawon shanu da aka gani yana ta yawo a kasuwa.

Sai dai, kungiyar Fulanin da ke kewayen kasuwar ta ki amincewa da matakin kame mutumin da ake zargin barawo ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace malamin addini a kokarin zuwa binne mahaifiyarsa, sun sace wasu 15

Bayanin mai magana da yawun ‘yan sandan Sokoto

A halin da ake ciki, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce an kama mutanen biyu ne a safiyar Lahadi 21 ga watan Afrilun 2024.

Da yake yawabi ga jaridar Punch, ya ce:

“Mun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin Gada a safiyar yau. An kama mutanen biyu da bindiga da shanu uku.
“Sun fito ne daga wani kauye a karamar hukumar Goronyo a jihar kuma ta hanyar binciken farko da muka yi, sun amsa laifinsu.
"Sun kuma yi alkawarin ba da cikakken bayani game da wadanda ake zarin sun gudu wanda muke fatan za a iya kama su tare da hukunta su a dokance."

An kashe sojoji a Arewacin Najeriya

A wani labarin, hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta shida a wani harin kwantan bauna da aka kai masu a kauyen Karaga da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Kara karanta wannan

An damke mutane sun yi karyar an yi garkuwa da su, sun bukaci fansar miliyoyin kudi

An kashe sojojin shida daga shiyya ta daya ta sojojin da aka tura a Allawa da Erena, a yayin da suka fita wani wani sintiri na yaki a yankin.

Sai dai sun fafata da 'yan ta'addan kuma sun kashe da dama daga cikinsu tare da jikkata wasu kafin suka amsa kiran mahaliccin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel