Najeriya Ta Takaita Fitar da Wutar Lantarki Zuwa Kasashen Benin, Nijar da Togo

Najeriya Ta Takaita Fitar da Wutar Lantarki Zuwa Kasashen Benin, Nijar da Togo

  • Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta takaita samar da wutar lantarki ga kasashen Benin, Niger, da Togo
  • Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke bin kasashen bashin Naira biliyan 132.2 na kudin wutar lantarki daga 2018 zuwa 2023
  • Hukumar NERC ta kuma ce takaita tura masu wutar zai taimakawa wajen wadatar da samuwar wutar a cikin gida Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Najeriya, ta ba da umarnin takaita samar da wutar lantarki ga abokan huldar dake kasashen Benin, Nijar, da Togo.

Najeriya ta takaita tura wutar lantarki zuwa kasashen waje
Hukumar NERC ta takaita tura wutar lantarki zuwa jamhuriyar Benin, Nijar da Togo. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Najeriya ta takaita fitar da lantarki

Hukumar da ke sa ido kan harkokin wutar lantarkin, watau System Operator, wani sashe da ke cikin kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya ne aka ba wannan umarni.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Kotun Kano ta dakatar da karbar sabon kudin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umurnin, na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken "Umarni na wucin gadi kan rarraba wutar lantarki a kan iyakoki, da batutuwa masu alaka," jaridar Leadership ta ruwaito.

Umarnin NERC, wanda aka buga a ranar Juma’a, 3 ga Mayu kuma ya fara aiki daga 1 ga Mayu, 2024, na dauke da sa hannun shugaban hukumar, Sanusi Garba, da mataimakinsa, Musiliu Oseni.

Wa'adin takaita tura wutar lantarki

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa a halin yanzu Najeriya na samar da wutar lantarki ga kasashen makwabta da suka hada da Jamhuriyar Benin, Nijar da kuma Togo.

Hukumar NERC ta ce za a takaita rarraba wutar zuwa kasashen ne na watanni shida, da kuma yiwuwar tsawaita wannan wa'adin.

NERC ta jaddada cewa yarjejeniyar wutar lantarki tsakanin ƙasashen duniya da na kamfanonin rarraba wuta na Najeriya na gaza cimma muradun masana'antar lantarki a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin kawo hanyar da za ayi sallama da matsalar lantarki

Ana bin kasashen bashin kudin wutar lantarki

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar rashin karbar kudaden wutar lantarki da ta turawa kasashen a tsawon shekaru, rahoton Arise News.

Ana bin wadannan kasashe bashin Naira biliyan 132.2 na kudin wutar lantarki da aka tura musu daga shekarar 2018 zuwa farkon shekarar 2023.

Umarnin wucin gadi na NERC akan takaita tura wuta ga abokan ciniki na waje na tsawon watanni shida zai kuma bunkasa tasirin samar da wutar ta cikin gida.

IPOB za ta kori kamfanin EEDC

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito kungiyar masuy fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta yi barazanar korar kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu daga Kudu maso Gabas.

Kungiyar IPOB ta yi wannan barazanar ne yayin da take korafin yadda yankin ke fama da rashin wutar lantarki alhalin al'uma na biyan kudin wutar ga kamfanin EEDC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel