Wa Ke Jagorantar Najeriya Yanzu? Atiku Ya Tambaya Yayin da Shettima Ya Tafi Amurka

Wa Ke Jagorantar Najeriya Yanzu? Atiku Ya Tambaya Yayin da Shettima Ya Tafi Amurka

  • Atiku Abubakar ya yi magana kan ziyarar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zuwa Amurka alhalin Bola Tinubu ba ya kasar
  • Atiku, dan takarar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya ce abin damuwa ne ace babu jagora a kasar yanzu
  • Ya yi nuni da cewa bai kamata ace Tinubu da Shettima su tsallake su bar kasar su a lokacin da al’ummar kasar ke fuskantar kalubale

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ziyarar da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kai Amurka, domin halartar taron kasuwanci ya bar gibi a shugabancin Najeriya.

Wannan kuwa ya faru ne kasancewar har yanzu Shugaba Bola Tinubu bai dawo Najeriya ba, kwanaki shida bayan halartar taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a Saudiya.

Kara karanta wannan

"Babu laifin Tinubu": Mataimakin kakakin majalisa ya magantu kan matsin tattali

Ziyarar Shettima zuwa Amurka ta haifar da gibi a shugabancin Najeriya
Atiku Abubakar ya magantu kan yadda Shettima da Tinubu suka bar Najeriya babu jagora. Hoto: @officialSKSM, @atiku
Asali: Twitter

Barin wannan babban gibi na shugabanci a Najeriya ya jawo hankalin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2023 da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wa yake jagorantar Najeriya?" - Atiku

Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan yadda aka bar Najeriya babu jagoranci alhalin kasar na fama da matsalolin tsaro da ke bukatar daukar matakai akai-akai.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, Atiku ya ce ana ta yi masa magana kan rashin shugaban kasa da mataimakinsa a fadar gwamnatin kasar.

"Ya zama abin damuwa yadda shugabannin biyu za su tsallake su bar kasar su a lokaci daya, musamman a yanzu da al’ummar kasar ke fuskantar kalubale masu yawa.
Tambayar da ke zuwa a zuciyata ita ce, wane ne ke jagorantar gwamnati a wannan lokaci, ko kuma daidai ne a ɗauka cewa muna kan jirgin da babu direba?"

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi wanda ya 'jawo' tabarbarewar tattalin arziki lokacin Buhari

- Atiku Abubakar

Tinubu bai dawo daga Saudiya ba

Har yanzu dai shugaba Bola Tinubu bai dawo Najeriya ba, kwanaki bakwai bayan kammala taron tattalin arzikin duniya na WEF da aka gudanar a kasar Saudiyya.

A yayin da aka ba ta tabbacin cewa sauran jami'an gwamnati da suka raka shugaban kasar zuwa Saudiya sun dawo Najeriya, shugaban bai dawo ba.

Sai dai wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasa ta shaidawa jaridar Businessday cewa shugaban ya tafi kasar Ingila ne saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba

Babban jami’in fadar shugaban kasar da ba ya son a bayyana sunansa ya lura cewa “shugaban ya saba yin hutun bayan irin wadannan tarurrukan.”

Amurka za ta girke sojoji a Najeriya?

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta karyata rahoton cewa Amurka, da Faransa za su kafa sansanonin sojoji a Najeriya.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, a sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ya ce labarin da ake yadawa kan kafa sansanonin karya ce kwai aka shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel