Kamfanin NNPC Ya Shawo Kan Matsalar da Ta Kawo Dogon Layi a Gidajen Mai

Kamfanin NNPC Ya Shawo Kan Matsalar da Ta Kawo Dogon Layi a Gidajen Mai

  • Biyo bayan wahalar mai da ta kunno kai a Najeriya, kamfanin NNPC ya yi bayani a kan abin da ya haifar da damuwar
  • Kamfanin ya kuma bayyanawa 'yan Najeriya matakan da ya dauka domin magance matsalar cikin gaggawa
  • Jami'in sadarwa na kamfanin, Olufemi Soneye, ya bada shawara ga 'yan Najeriya a kan yadda za su mu'amalanci matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kamfanin albarkatun mai na Najeriya (NNPC) ya ce ya yi nasarar shawo kan matsalar da ta haifar da karancin mai a cikin satin nan.

Fuel statiom
Kamfanin NNPC ya ce ya magance matsalar wahalar man fetur. Hoto: George Osodi
Asali: Getty Images

Abin da ya jawo wahalar man fetur

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa jami'in sadarwa na kamfanin Olufemi Soneye ne ya bayyana hakan ga 'yan Najeriya a jiya Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Hukumar 'yan sanda ta yi karin haske kan rade radin kai hari a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin na NNPC ya bayyana cewa jigilar kayayyaki ne ya haifar da matsalar kuma tuni an magance ta.

NNPC ya kara kudin man fetur?

Dangane da karin kudin mai da aka samu a wasu gidajen mai kuma, Mista Olufemi Soneye ya ce kamfanin bai kara farashi ba, cewar jaridar Vanguard

Ya kuma shawarci 'yan Najeriya a kan cewa su guji sayan mai domin tanadi saboda akwai wadatattaccen mai a ƙasar.

Ga abin da yake cewa:

"Kamfanin NNPC yana sanar da 'yan Najeriya cewa karancin man fetur da aka samu a wasu sassan Najeriya yana da alaka ne da matsalolin jigilar kayayyaki kuma an riga an magance matsalar."

- Olufemi Soneye, jami'in sadarwa na NNPC

Rahotanni sun tabbatar da cewa karancin mai din ya jefa mutane cikin damuwa da kuma haifar da dogayen layuka a gidajen mai a birane da dama.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Yadda ’yan Najeriya za su iya yin karatu kyauta a kasar Birtaniya

A jihar Kaduna an ruwaito cewa 'yan bumburutu suna sayar da litar mai a kan ₦1,000 yayin da gidajen mai da dama suka kulle.

Fetur: Dokar ta ɓaci ta fara aiki a Jigawa

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, gwmnatin jihar Jigawa ƙarƙashin gwamna Umar Namadi ta kafa dokar kar-ta-kwana kan gidajen mai.

Ana sa ran cewa dokar za ta tabbatar da wadatan mai a fadin jihar tare da hukunta 'yan kasuwa da suke rufe gidajen mai ba tare da dalili ba.

Tuni dai dokar ta fara aiki jiya Alhamis, 25 ga watan Afrilu inda aka ruwaito cewa membobin kwamitin sun fara zaga gidajen mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel