Kashim Shettima Ya Soke Tafiya Zuwa Amurka Saboda Matsalar Jirgi, An Tura Minista

Kashim Shettima Ya Soke Tafiya Zuwa Amurka Saboda Matsalar Jirgi, An Tura Minista

  • Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kuwanci a Dallas
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya soke wannan tafiya ne sakamakon wata tangarɗa da jirginsa ya samu, ministan waje zai wakilci Tinubu a taron
  • Hadimin shugaban ƙasa ya ce a yanzu Shettima zai koma bakin aiki, ya ci gaba da ayyukan gwamnati gabanin dawowar Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai yi zuwa ƙasar Amurka domin halartar taron kasuwanci a birnin Dallas.

Shettima ya soke tafiyar wanda zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron da za a tattauna harkokin kasuwanci tsakanin Amurka da nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Mutane sun gudu yayin da ƴan bindiga suka kai hare hare a garuruwa 10 a Kaduna

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Kashim Shettima.ya fasa halartar taron kasuwanci a Dellas Hoto: Kashim Shetima
Asali: Facebook

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin midiya da sadarwa, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata sanarwa a X ranar Litinin, 6 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya zauna, Minista zai wakilci Tinubu

Hadimin ya ce a halin yanzu ministan harkokin ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ne zai wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu a taron wanda zai gudana a Dallas.

Nkwocha ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasar wanda tun asali aka tsara zai wakilci Tinubu a taron ba zai samu zuwa ba saboda matsalar da jirginsa ya samu.

Matsala ta jawo Kashim Shettima ya fasa

Ya ce:

"Hakan ta faru ne sakamakon tangardar na'ura da jirgin mataimakin shugaban ya samu, wanda ya tilasta masa fasa tafiyar bisa la'akari da shawarin da aka ba shi."

Ya kuma kara da cewa mataimakin shugaban kasar zai cigaba da gudanar da wasu ayyuka na kasa bayan fasa wannan tafiya zuwa Amurka.

Kara karanta wannan

"Da yawa ba su da muƙamai": Jigon APC ya magantu kan zargin rikicin Tinubu da El-Rufai

Shugabannin da za su je taro a Amurka

Daga cikin shugabannin kasashen Afirka da ake sa ran za su je taron sun hada da shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai, shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera da shugaba Joao Lourenco na Angola.

Sauran sune shugaba Mokgweetsi E.K. Masisi na Botswana, Shugaba José Maria Neves na Cabo Verde, da mataimakin Firaministan Lesotho, Nthomeng Majara.

Taron kasuwancin zai maida hankali ne kan karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da kuma gano hanyoyin zuba jari tsakanin Amurka da kasashen Afirka.

Gwamna Fubara na cikin matsala

A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ribas ta sake bijirewa Gwamna Siminalayi Fubara a karo na uku cikin watanni uku.

Majalisar ta kuma yi barazanar cewa za ta ɗauki tsattsauran mataki kan Gwamna Fubara idan ya ci gaba da yin watsi da dokokin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel