Kano: An Karrama Yaro Dan Shekara 16 da Kujerar Hajji Saboda Kur’ani

Kano: An Karrama Yaro Dan Shekara 16 da Kujerar Hajji Saboda Kur’ani

  • An karrama yaron da ya nuna hazaka a kan hadda da sanin ma'anonin Alkur'ani a jihar Kano da kujerar zuwa aikin Hajji
  • Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ce ta bayyana kyautar tare da bayyana dalilai da suka sa aka karrama mahaddacin
  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ji jawabi mai ratsa zuciyia kan bajintar da wannan yaron ya nuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yaro dan shekara 16 a jihar Kano mai suna Ja'afar Yusuf ya samu damar zuwa aikin Hajjin bana saboda kwarewa a karatun Alkur'ani.

Rahotanni sun nuna cewa an karrama yaron ne sabod haddar Alkur'ani cikakkiya da yake da ita tare da sanin ma'anonin kalmomina.

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

Kano state government
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dole a cigaba da karfafan yara irinsa. Hoto: Kano State Pilgrims Welfare Board
Asali: Facebook

Hukumar jin dadin aljazai ta jihar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa gwamnatin jihar ne ta karrama shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karrama yaro mai haddar Kur'ani

A lokacin da yake bayyana kyautar, darakta a hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Laminu Danbappa, ya ce yaron ya nuna bajinta sosai.

A cewarsa hukumar ta ba wa yaron kyautar ne saboda kwarewarsa a fannin karatun Alkur'ani abin a yaba ne matuka.

Ya kara da cewa yaron ya fahimci dukkan ma'amonin kalmomin Alkur'ani tare da sanin a surar da kowace kalma ta take.

Jawabin gwamnan jihar Kano

A cewar jami'in yada labarai na hukumar, Sulaiman Dederi, gwaman jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da kansa ya yabawa yaron ya kuma ce ya zamo abin misali ga sauran al'umma.

A cewar gwamnan, hazakar da yaron ya nuna tana bayyana irin jajircewa da lura da addini da aka san mutanen Kano da ita.

Kara karanta wannan

Muna kashe N1.2bn a duk wata domin samar da ruwa a Kano, in ji gwamnatin Abba

Sannan ya kara da cewa akwai muhimmanci sosai wurin karfafawa yara masu hazaka gwiwa domin samar da manyan gobe masu nagarta.

Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa alhazai

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyacin aikin hajjin 2024 a jihar

Gwamna Yusuf ya ce tallafin N500,000 zai shafi wadanda suka biya Naira miliyan 4.9 na farko kuma aka bukaci su biya karin Naira miliyan 1.9

Asali: Legit.ng

Online view pixel