Kotu Ta Saka Ranar Cigaba da Sauraron Shari’ar Abduljabbar Kabara a Kano

Kotu Ta Saka Ranar Cigaba da Sauraron Shari’ar Abduljabbar Kabara a Kano

  • Babbar kotun musulunci da ke birnin Kano ta ayyana ranar cigaba da sauraron ɗaukaka karan da Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar
  • Kotun ta yanke hukuncin ne a safiyar yau Litinin, 6 ga watan Mayu bayan jami'an gidan gyaran hali sun kawo malamin kotu
  • Yanzu dai malamin zai cigaba da zama a gidan gyaran hali har sai ranar da alkalin ya saka domin cigaba da sauraron karar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Babbar kotun shari'ar Muslunci da ke sakatariyar Audu Bako ta saurari ɗaukaka karar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi.

Abduljabbar Nasiru kabar
Kotu ta saka ranar cigaba da sauraron karar Abduljabbar. Hoto: UGC
Asali: UGC

Za a cigaba da shari'ar Abduljabbar Kabara

Bayan sauraren karar, alkalin kotun ya sanya ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu a matsayin ranar cigaba da sauraron ɗaukaka kakar, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hukumar UBEC za ta yi horo na musamman ga malamai 1480

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoton da gidan radiyon Freedom da ke Kano ya wallafa a shafinsu na Facebook ya nuna cewa da safiyar yau ne jami'an gidan gyaran hali suka kawo malamin gaban kotu.

Abduljabbar Nasiru Kabara ya dauka kara ne biyo bayan hukuncin kisa da wata kotu ta yanke masa a watannin da suka gabata.

Laifin da ake zargin Abduljabbar da aikatawa

Kotun ta yanke wa malamin hukuncin kisa ne bisa zarginsa da yin batanci ga annabi Muhammad (SAW) a cikin karatunsa.

Amma sai dai ya kalubalanci hukuncin kotun ta inda ya nuna shi sam bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Hakan ya sa aka tsare shi a gidan gyaran hali domin ba shi lokacin daukaka kara kafin a zartar masa da hukuncin.

Mukabalar Abduljabbar da sauran malamai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta shirin korar wadanda Ganduje ya dauka aiki

Tun farko dai wasu malamai ne a birnin Kano suka kalubalanci Abduljabbar Nasiru Kabara da yi wa Annabi Muhammad (SWA) batanci.

Hakan ya sanya malamin ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta wancan lokacin ta haɗa mukabala tsakaninsa da malaman da suke ganin ya yi kuskure.

Daga bisani gwamnatin jihar ta wancan lokacin karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta shirya mukabala tsakanin malaman da Abduljabbar Nasiru Kabara.

Sakamakon mukabalar Abduljabbar Kabara da malamai

Sakamakon mukabalar ya nuna cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya kasa kare kansa daga zargin da ake masa.

Bayan ya amsa laifin sai daga baya ya bada sanarwar cewa sam bai aminta da sakamakon mukabalar ba.

Hakan ya sa aka kai shi gaban alkali wanda aka yanke masa hukuncin kisa bayan sauraron shari'ar na tsawon lokaci.

Daliban Abduljabbar sun jefi malamai da zargi

A wani rahoton, kun ji cewa daliban Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun zargi wasu malamai da hada kai don kawo cikas a shari’ar da ake yi da malaminsu.

A farko an tasa keyar Abduljabbar zuwa kotun Musulunci inda aka yanke masa hukuncin kisa, daga bisani ya daukaka kara zuwa babbar kotu da ke jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel