Abba Gida Gida ya Kaddamar da Titi Mai Hawa 3 kan Kudi ₦15bn a Dan Agundi

Abba Gida Gida ya Kaddamar da Titi Mai Hawa 3 kan Kudi ₦15bn a Dan Agundi

  • Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ginin titin sama a kan ₦15bn a titin 'Dan Agundi domin rage cunkoson abubuwan hawa a yankin
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da titin mai hawa uku a ranar Lahadin nan domin ganin yadda za a fara gudanar da aikin
  • An ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin kuma ana sa ran zai kammala kwangilar titin zamanin a cikin watanni goma sha takwas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya dora tubalin ginin titin saman da kudinsa ya kai Naira Biliyan 15 a wuraren Kofar 'Dan Agundi a kwaryar birnin Kano.

Kara karanta wannan

'Akwai manyan da ke yi wa gwamnatina makarkashiya', Gwamnan APC ya koka

Gwamnati ta bawa kamfanin CCG Nigeria Limited kwangilar aikin da ake sa ran kammalawa cikin watanni goma sha takwas domin rage cunkoson ababen hawa a yankunan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamanatin Kano ta kaddamar aikin titin Dan Agundi kan N15bn Hoto: Sanusi Bature DTofa
Asali: Facebook

A sakon da Sanusi Bature Dawakin Tofa, darakta janar na gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, kammala titin zai kawo ci gaba a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za a gama aikin da wuri," Wang

Yayin kaddamar da aikin titin mai hawa uku, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa na ayyukan raya kasa a fatansa na mayar da Kano babban birni.

Ya ce ya bayar da wasu kwangilolin manya-manyan titunan a Tal'udu a kokarin rage cunkoso, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

"Mun samar da wasu hanyoyin da masu ababen hawa za su bi a kokarin bin dokokin aikin da kuma tsare masu amfani da titunan."

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

A jawabinsa, Manajan ayyuka a kamfanin CCG Nigeria Limited, Mista Gee Wang ya yi alkawarin kammala aikin cikin watanni sha takwas din aka tsara tun da fari.

Za a gina titin Kano a watanni 4

Mun ruwaito muku cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar gina Western bypass ga kamfanin Dantata and Sawoe, inda gwamnatin ta yi gargadin a kammala aikin da wuri.

Ministan Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub ya ce za a kammala aikin cikin watanni hudu saboda an samar da dukkanin abubuwan da ake bukata wajen gudanar da aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel