Abuja: ’Yan Sanda Sun Cafke Manyan ’Yan Fashin da Suka Fitini Birnin Tarayya

Abuja: ’Yan Sanda Sun Cafke Manyan ’Yan Fashin da Suka Fitini Birnin Tarayya

  • Yan sandan sun cafke shugaban 'yan fashin ne ne biyo bayan kamo wani abokin cin mushen shi a watan Fabrairu
  • Dukkan barayin sun amsa laifin su na fitinan birnin tarayya Abuja da sace-sace da fashi da makami
  • Ƴan Sanda sun bayyana irin muggan makaman da barayin ke aiki dasu wurin aikata ayyukan ta'addanci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Rundunar 'yan sanda a birnin tarayya, Abuja, sunyi nasarar cafke Chukwumeka Oputa, kasurgumin barayon da ya fitini birnin.

A wani jawabi da rundunar 'yan sandan suka fitar a Facebook aka fahimci haka.

Inspector General of Police
Manyan barayin sun amsa laifin su na sace-sace da fashi da makami a birnin tarayya Abuja. Hoto: NIgerian Police Force Asali: Facebook
Asali: Facebook

Babban barawon mai shekara 38 shugaba ne na 'yan fashi da makami da sauran munanan laifuka a Abuja.

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta bayyana cewa ta kamashi ne biyo bayan kama abokin cin mushen shi, Moses Hassan.

Hukumar 'yan sandan tayi nasarar kama Moses Hassan din ne ranar 14 ga watan Fabrairu.

Yadda aka kamo sauran barayin a Abuja

Hukumar yan sandan birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa bayan bincike mai zurfi tayi nasarar kama wasu barayi guda uku.

Ragowar sauran wadanda ake zargin barayi ne sun hada da Praise Etta, Rafeal Dav da Thomas Akange.

Rahoton yayi nuni da cewa suma suna hada kai ne da shugaban kungiyar tasu, Chukwumeka Oputa, don aikata ayyukan ta'addanci.

Abuja: Barayin sun amsa laifin su

'Yan fashi da makamin sun tabbatar da cewa suna ta'addancin ne karkashin kungiyar asiri ta Vikings.

Kuma dukkan su sun amsa laifin su na aikata fashi da makami da sace-sace a cikin da wajen Abuja.

Kara karanta wannan

Rikici da malamin addini: Dr Idris Dutsen Tanshi ya dawo Bauchi bayan gudun hijirar kwanaki

Makaman da aka kama tare dasu

Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya, CP Benneth IGweh, ya bayyana irin muggan makamai da suka kama a hannun barayin.

Makaman sun hada da AK47 guda hudu, bindigogin gargajiya guda uku da tarin harsashi.

Kiran shugaban 'yan sanda ga 'yan Abuja

Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya ya kira al'umma da su rika basu bayanai idan suka ga motsin bata gari.

Jami'in ya kuma jaddada kokarin su na tabbatar da dakile ayyukan barna a Abuja babu dare babu rana.

An kama babban dan bindiga a Abuja

A wani rahoton kuma, Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Sa’idu Abdulkadir.

Sunyi nasarar kamun ne bayan wani samame da suka kai a sansanonin masu garkuwa da mutane da ke kan iyaka da Nasarawa da Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel