Cin Zarafin Daliba: Mahukunta Sun Garkame Makarantar Lead British a Abuja

Cin Zarafin Daliba: Mahukunta Sun Garkame Makarantar Lead British a Abuja

  • Biyo bayan bidiyon cin zarafin daliba da ya yadu a soshiyal midiya wanda ya tayar da hankalin jama'a, an rufe makarantar Lead British
  • Mahukuntan makarantar sun ba da sanarwar dakatar da karatu na kwanaki uku domin ba su damar yin bincike mai zurfi kan lamarin
  • A zantawar Legit Hausa da wasu daga cikin ɗaliban da ke karatu a sakandare, sun ce cin zarafin dalibai ya fi muni a makarantun gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar makarantar Lead British da ke Abuja, ta garkame makarantar biyo bayan bidiyon cin zarafin wata daliba ya karade shafukan sada zumunta.

An rufe makarantar Lead British ta Abuja
Abuja: An rufe makarantar Lead British biyo bayan rahoton cin zarafin daliba. Hoto: @mooyeeeeeee
Asali: Twitter

Wata mai amfani da shafin X @mooyeeeeeee ce ta wallafa bidiyon yadda wata daliba ke cin zarafin wata daliba ta hanyar sharara mata mari.

Kara karanta wannan

Yadda matsalar ruwa ke haifar da wahalar rayuwa a Arewacin Najeriya

Dalilin rufe makarantar Lead British a Abuja

Bidiyon ya haifar da tsokacin dubban masu amfani da soshiyal midiya wadanda suka yi kira ga hukumomin makarantar da su binciki lamarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taro da suka yi a ranar Talata, mahukuntan makarantar sun ba da sanarwar dakatar da karatu na kwanaki uku don ba su damar yin bincike mai zurfi kan lamarin.

Wani babba a mahukuntan ya ce matakin rufe makarantar na wani dan lokaci yana da amfani ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa.

Makarantar Lead British ta magantu

Jaridar Vanguard ta ruwaito Abraham Ogunkambi, shugaban makarantar Lead British Abuja, ya fitar da wata sanarwa a ranar Talata, dangane da lamarin.

Ogunkambi ya bayyana rashin jin dadi da kuma Allah wadai da makarantar ta yi kan abin da ya faru da dalibar tare da bada tabbaci kan gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

FAAN ta dauki matakin gaggawa da gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

Ya kara da cewa tuni makarantar ta tuntubi dalibar da da kuma iyayenta, inda suka dauki matakin tattaunawa da yarinyar domin ganin ba ta fada mummunan yanayi ba.

Cin zarafin dalibai a makarantun gwamnati

A zantawar Legit Hausa da wasu daga cikin ɗaliban da ke karatu a makarantun sakandare, sun ce cin zarafin dalibai ya fi muni a makarantun gwamnati.

Wani dalibi Abubakar Bello, ya ce shugabannin dalibai (siniyas) na azabtar da na kasa da su fiye da hankali, inda ya buga misali da shi karan kansa.

"An taba yi muna bulala 100 ni da abokina, har gobe ina yi wa siniyan Allah ya isa saboda bamu san laifin da muka yi ya yi mana duka haka ba."

Wani tsohon dalibin makarantar sakandare ta Bindawa, Yusuf Bature, ya ce ba zai manta wani hukunci da wani siniya ya yi masa ba, wanda sai da ya koma gida saboda hakan.

"Lebo prifet din mu ya aike ni debo ruwa, na je na tarar da layi a famfon, tun bayan magariba har aka kusa shiga ajin dare ban samu ruwan ba, tunda ana tsayawa dibar na Sallah.

Kara karanta wannan

Jami'ar Najeriya ta dauki mataki kan malamin da aka kama yana lalata da daliba

"Ai kuwa muna cikin ajin dare ya zo nema na, ya tambayi bokiti na ce na barshi a layi. Wallahi tun daga aji har wajen famfo ina tafiya da guiwowina a kasa, jini kawai ke zuba."

Bidiyo: Matar aure na neman haihuwa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wata matar aure ta dauki bidiyon kanta rike da kayan jarirai tana sharbar kuka tare da yin addu'ar Allah ya bata haihuwa.

An ruwaito cewa matar na fuskantar hantara da mulakanci daga mutane sakamakon jinkirin da ta samu na samun haihuwa. Tuni 'yan Najeriya suka yi martani kan bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel