Ta sharara wa malamar makaranta mari, an tisa keyar ta zuwa gidan yari
- Kotu ta yanke hukuncin zaman gidan yari ne shekara daya ga wata mata da ta nakada wa malaman makaranta duka
- Matar da shararawa malamar mari ne kuma ta rika fizgar gashin kanta a gaban yara da dalibai a dalilin cewa ta ga wani kulu a kan diyar ta
- Hukuncin ta kotun ta yanke ya bawa lauyar matan mamaki inda ya yi ikirarin cewa kotun ta yi hakan ne saboda matsin lamba da ta ke fuskanta daga malaman makarantar
Wata kotu a kasar Faransa ta garkame wata mata har na tsawon shekara daya saboda mari da kuma duka da ta nakada wa malamar daya daga cikin yayan ta bayan ta lura da wani kulu a kan diyar na ta.
A cewar mai shigar da kara, kotun da ke garin Mably na kusa da Roanne ya tsananta hukuncin fiye da yadda dokar kasar ta tanadar wanda bai kamata ya wuce watanni shida ba.
Matar mai suna Elizabeth Elmaz ta shararawa shugaban makarantar frimarin da diyar ta take zuwa mari tare da fizgar gashin kanta a gaban yara, iyayen yara da sauran malamai.
KU KARANTA: Gwamnati ta ware N800m don koyar da larabci da addinin musulunci - Minista
Lauya mai kare matar, Hugues Roumeau ya bayyana hukuncin a matsayin abin takaici kuma ya zargi kotun da yin hakan ne saboda irin matsin lambar da alkalin ya samu daga malamai da suka rika zanga-zanga a wajen kotun tare da neman kotun tayi hukuncin da zai zama darasi ga sauran iyaye.
Kamar yadda jaridar Le Progress ta ruwaito, an aike da Elmaz mai shekaru 28 zuwa gidan yarin a wajen garin Saint-Etienne mai nisan kilomita 90 daga birnin Mably.
Elmaz ta bayyana wa kotu cewa dukan da tayi malaman yunkurin kare kanta ne amma sauran shedu da aka gabatar sun karyata hakan. Lauyan Elmaz ya ce kotun bata bawa Elmaz tapinta ba amma kuma bai bayyana cewa ko zata daukaka kara ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng