Hukumar JAMB Ta Dauki Mataki Kan Wasu Jami’anta da Suka Ci Zarafin Daliba Mai Hijabi

Hukumar JAMB Ta Dauki Mataki Kan Wasu Jami’anta da Suka Ci Zarafin Daliba Mai Hijabi

  • Yayin da wasu jami’an hukumar JAMB suka bukaci wata daliba sanye da hijabi da ta cire yayin tantancewa, an dauki mataki a kanta
  • Hukumar ta tabbatar da cewa ta dauki matakin ne domin ya zama izina ga sauran jami’anta da ke shirin aikata haka a nan gaba
  • Hakan ya biyo bayan bukatar wata daliba Musulma cire hijabi yayin tantancewa a jihar Legas wanda hakan ya sabawa dokar hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos Hukumar Jarrabawa ta JAMB ta dauki mataki kan jami’anta da suka ci zarafin wata daliba sanye da hijabi.

Lamarin ya faru ne a makarantar Bafuto da ke tashar mota ta Ile-Iwe a Ejigbo da ke jihar Legas a Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yayin da ake zarginsa da sulalewa da Yahaya Bello, Gwamna ya roki Tinubu alfarma

Hukumar JAMB ta ladabtar da jami'anta kan tilasta daliba cire hijabi
Hukumar JAMB ta tabbatar da daukar mataki kan wasu jami'anta da suka bukaci daliba ta cire hijabi. Hoto: JAMB.
Asali: Facebook

Hukumar JAMB ta koka kan halin jami'an

Daraktan yada labaran hukumar, Dakta Fabian Benjamin shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 21 ga watan Afrilu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benjamin ya ce abin takaici ne yadda lamarin ya faru saboda jami’an basu mai da hankali kan abin da ya kamata ba yayin tantancewar.

Ya ce kuma jami’an sun jahilci dokokin hukumar yayin tantancewa inda ya ce hukumar ba ta ji dadin yadda lamarin ya kasance ba.

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, jami’an hukumar sun bukaci dalibar ta cire hijabinta yayin da ake tantancewa kafin shiga dakin jarrabawar.

The Guardian ta ce daga bisani an ba dalibar damar shiga dakin jarrabawar bayan tantance ta da hijabinta.

“Duk da jahiltar dokokin hukumar ba hujja ba ne, an hukunta jami’an da suka aikata haka saboda ya zama izina ga saura da suke da niyyar aikata haka.”

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta rage farashin mai ne saboda rashin inganci? Gaskiya ta fito

“Ya kamata a sani cewa wannan hukuma ce ta kasa baki daya da bata da wani tsari na hana kowa sanya wani abu da ke da alaka da addini ba wanda hakan ya sha faruwa a Najeriya.”

- Fabian Benjamin

An shawarci dalibai masu rubuta JAMB

A wani labarin, kun ji cewa an shawarci daliban da ke shirin rubuta jarrabawar JAMB da su zauna cikin shiri.

Wani masani kan rubuta jarrabawar wanda ya dade ya na taimakawa dalibai, Osunwoye Samuel ya bukaci daliban su mai da hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel