Jami’ar Najeriya Ta Dauki Mataki Kan Malamin da Aka Kama Yana Lalata da Daliba

Jami’ar Najeriya Ta Dauki Mataki Kan Malamin da Aka Kama Yana Lalata da Daliba

  • Jami'ar Najeriya ta Nsukka (UNN) ta dakatar da wani malami, Okwunka Omeaku da ake zargin an kama shi a bidiyo yana lalata da wata daliba
  • A halin yanzu dai hukumar gudanarwar makarantar ta kafa kwamiti da zai yi bincike kan lamarin domin daukar matakin da ya dace
  • A cikin wata sanarwa da jami'ar ta fitar, ta ce ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen yi wa Omeaku hukunci mai tsanani idan aka same shi da laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Enugu - Hukumar gudanarwar jami’ar Najeriya ta Nsukka (UNN) da ke jihar Enugu ta dakatar da Mfonobong Udoudom, wani malami a sashen 'Ilimin bai daya'.

Kara karanta wannan

Cin zarafin daliba: Mahukunta sun garkame makarantar Lead British a Abuja

Jami'ar Najeriya ta fara bincike kan malamin da ake zargin ya yi lalata da daliba
Jami’ar UNN ta dakatar da malami saboda zargin yana lalata da dalibai
Asali: Facebook

Zargin lalata: Jami'a ta dakatar da Udoudom

Kakakin jami’ar UNN, Okwunka Omeaku, a ranar Talata, ya ce an dakatar da Udoudom ne bayan da aka kama shi a wani faifan bidiyo da ake zargin yana cin zarafin wata daliba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okwunka Omeaku ya ce jami'ar ba ta daga kafa kan abin da ya shafi lalata tsakanin malamai da dalibai, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A cewar sanarwar da kakakin jami'ar ya fitar:

“Dakatarwar da aka yi wa Udoudom ta fara aiki nan take har sai an samu sakamakon kwamitin ladabtarwa da jami’ar ta kafa domin yin bincike kan zargin.

UNN ta yi doka kan lalata a jami'ar

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, jami’ar ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta Udeudom idan kwamitin ya same shi da laifi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rage kudin makaranta yayin da ya ƙara albashin malamai, zai ba dalibai aiki

"UNN tana cikin jami'o'in kasar nan da ke da doka ta cin zarafi, wacce ke daidaita alakar da ke tsakanin malamai da dalibai da kuma tsakanin ma'aikatanmu maza da mata".
"A matsayinmu na jami'a, mun himmatu wajen kare dalibanmu daga duk wani nau'i na cin zarafi, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta Udoudom idan aka same shi da laifi."

- Okwunka Omeaku.

An kama malamin jami'ar UNN tsirara

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an zargi Mista Udoudom a ranar Litinin da yunkurin yin lalata da dalibar sa a ofishinsa.

An ce malamin ya sha alwashin cewa dalibar ba za ta taba tsallake darasin da yake koyarwa ba har sai ta mika kanta ya yi lalata da ita.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade soshiyal midiya, an ga yadda aka kama malamin tsirara amma daga baya aka ba shi damar sanya gajeren wando.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ta ta'azzara a Filato, an rufe jami'ar jihar bayan kashe dalibi

Cin zarafi: An rufe makaranta a Abuja

A wani labarin, mahukuntan makarantar Lead British da ke Abuja sun rufe makarantar na tsawon kwanaki bayan da aka yi zargin cewa an ci zarafin wata daliba.

Kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, an ga wata daliba tana cin zarafin wata daliba ta hanyar sharara mata mari da hantara, lamarin da ya jawo cece-kuce a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel