Ana Cikin Azumi Mutane Sun Fasa Rumbun Ajiya da Dasa Wawa Kan Kayan Abinci a Arewa

Ana Cikin Azumi Mutane Sun Fasa Rumbun Ajiya da Dasa Wawa Kan Kayan Abinci a Arewa

  • An dasa wawa kan kayan abinci da aka ajiye a rumbunan ajiya na gwamnati da ke unguwar Bayan Kara a birnin Kebbi
  • Mutanen da suka farmaki wajen dai sun yi awon gaba da kayayyakin abinci tare da fasa shagunan wasu ƴan kasuwa
  • Gwamnatin jihar ta bayyana. satar a matsayin abin takaici, inda ta ce kayan abincin an sayo su ne domin rabawa jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Wasu mazauna jihar Kebbi sun fasa wani rumbun ajiyar gwamnati da ke unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Mutanen dai sun dira a rumbun ajiyar ne a daren ranar Asabar tare da dasa wawa kan kayan abinci, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Miyagu sun kutsa kai har ofis, sun kashe babban malamin jami'ar Arewa

An fasa rumbun ajiya a Kebbi
Matasa sun wawashe kayan abinci a rumbun ajiyar gwamnati a Kebbi Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Yadda aka fasa rumbun ajiyar

Mutanen sun bijirewa jami’an tsaro da ke wurin, sun kuma fasa wasu shagunan ƴan kasuwa a yankin inda suka yi awon gaba da kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika sun dasa wawa kan wata babbar mota mai ɗauke da kayan hatsi iri-iri da ake son rabawa a Birnin Kebbi, rahoton Westernpost ya tabbatar.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya, shugaban ƙungiyar masu sayar da abinci a Kasuwar Bayan Kara a Birnin Kebbi, Muhammadu Gwadangwaji, ya ce wasu matasa sun ƙona wasu shaguna da rumbunan ajiya na ƴan kasuwa.

A kalamansa:

"Jami'an tsaro sun yi ta harba bindiga da barkonon tsohuwa a sama, amma matasan ba su tsorata ba. Sun shiga da ƙarfi sun kwashe kaya a rumbun ajiyar gwamnati da wasu shagunanmu."

Me gwamnati ta ce lamarin?

Da yake mayar da martani, babban sakataren yaɗa labarai na gwamna Nasir Idris, Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin "abin takaici".

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a jihohi 2 na Arewa, sun lalata sansaninsu

A kalamansa:

"Irin wannan lamari bai taɓa faruwa a Kebbi ba. Kayayyakin abincin da suka wawashe na daga cikin kayan abincin da gwamnatin jiha ta saya domin rabawa al’umma.
"Gwamnati ta sayo tare da raba hatsi iri-iri da suka kai sama da N5bn a cikin manyan motoci sama da 200. Abin baƙin ciki ne waɗanda suka kutsa cikin rumbun ajiyar sun je ne domin sace abin da mallakin mutanen jiha ne.

An fasa rumbun ajiya a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsageru sun fasa wurin ajiya na gwamnati da ke unguwar Gwagwa a birnin tarayya Abuja.

Biyo bayan aika-aikar fasa rumbun ajiyar na gwamnati, an sace kayan abinci na maƙudan kuɗaɗe daga ɗakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel