Gwamnatin Kano Ta Bayyana Muhimmin Shirin da TaKe Yi Wa Marayu da Nakasassu

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Muhimmin Shirin da TaKe Yi Wa Marayu da Nakasassu

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir ta fara shirye-shirye na musamman domin walwalar marayu da naƙasassu a jihar
  • Gwamnatin ta kuma kammala dukkanin tsare-tsaren da suka kamata domin tallafaa yaran da ke zaune a gidajen marayu
  • A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, za a ƙaddamar da hukumar naƙasassu a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara babban shiri domin tabbatar da walwalar marayu da naƙasassu a jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma kammala shirye-shiryen tallafawa yaran da ke zaune a gidajen marayu, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin kawo karshen matsalar

Gwamnatin Kano za ta faranta ran marayu
Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da nakasassu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A cewar sanarwar da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin jihar ta shirya ƙaddamar da hukumar naƙasassu, rahoton AIT ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane tallafi Gwamna Abba zai ba marayu?

Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Abba ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafawa mazauna gidajen marayu a Kano domin samun ingantacciyar rayuwa har zuwa girmansu.

A kalamansa:

"Wannan alƙawarin yana nuna ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samar da tsaro da walwala ga mazauna gidajen marayu."

Gwamnan ya kuma bayyana ƙudurinsa na magance matsalolin da suka shafe su ta hanyar samar da aikin yi, samar da guraben ƙaro karatu, samar da tallafin karatu, da bada tallafi wajen aurar da matan da ke zaune a gidajen marayu.

Hakan a cewarsa ya yi daidai da manufar gwamnati ta damawa da kowa wajen ganin an samu cin ribar romon dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta ɗauki mataki kan ɗan Kwankwaso da mutum 3 da Gwamna Yusuf ya naɗa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma bayyana shirin kafa wata hukumar kula da naƙasassu tare da yin alƙawarin ɗauko wani daga cikinsu ya jagoranceta.

Batun naɗa ɗan Kwankwaso kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da naɗin sababbin kwamishinoni huɗu waɗanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa mata.

Majalisar ta tantance kwamishinonin ne ciki har da ɗan Rabiu Musa Kwankwaso, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso a zamanta na ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel