Tinubu ya ba Ali Nuhu Mukami a Hukumar Fina-Finai Saboda Rarara? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya ba Ali Nuhu Mukami a Hukumar Fina-Finai Saboda Rarara? Gaskiya ta bayyana

  • Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana wa duniya cewa shi ne ya yi ruwa ya yi tsaki har Shugaban kasa ya ba Ali Nuhu mukami
  • Idan ba a manta ba, a watan Fabrairu ne Bola Ahmed Tinubu ya nada Ali Nuhu a kan kujerar shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya
  • Rarara ya ce ya yi murna da wannan mukami, sai dai har yanzu gwamnatin Tinubu ba ta saka masa ba akan hidimar da ya yi a zaben 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Shugaba Tinubu, ya fitar da sanarwa nada Ali Nuhu matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Barazanar kisa: Gwamnan PDP a Arewa ya ba Remi Tinubu hakuri, ya daukar mata alkawari

Mutane da dama sun musamman jarumai da ma'aikata a masana'antar fim ta Kano (Kannywood) sun yi murna kan wannan nadi, ko ba komai "namu ya samu."

Rarara ya taimakawa Ali Nuhu
Dauda Rarara ne silar ba Ali Nuhu mukamin shugaban hukumar fina-finai. Hoto: Ali Nuhu Mohammed, Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

Ba wai a iya taka rawa a fina-finai kadai ya tsaya ba, Ali Nuhu yana da shaidar karatu a fannin hada fim daga jami'ar California da kwalejin ilimin isar da sako da ke New Delhi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Nuhu ya samu muƙami sila ta - Rarara

Jaridar Leadership Hausa ta ruwaito shahararren mawakin siyasar, Dauda Kahutu Rarara, ya ce:

"Ba ko shakka, ni ne nan nayi ruwa nayi tsaki har Allah ya nufa Shugaba Bola Tinubu ya ba Ali Nuhu muƙamin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.
"Nayi matukar farin ciki da aka ba Ali Nuhu wannan mukami, domin sai da muka shiga muka fita sannan wannan mukami ya tabbata."

Kara karanta wannan

N585m: Jama'a sun taso EFCC da Tinubu a gaba saboda an ji tsit a binciken Edu

Tinubu ya biya Rarara wahalar 2023?

Premium Times ta ruwaito Rarara yana tsokaci game da shugabancin Bola Tinubu, musamman a bangaren hidimar da ya yi a zaben 2023 ko an saka masa, ya ce:

"Mukamin da aka ba Ali Nuhu bai isa ya zama ma'auni na an biyani aikin da na yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba.
"Duk da cewa na yi farin ciki da wannan muƙamin da aka ba shi, amma ko kusa wannan abu ba zai zama dalilin da zai sa na ce an biya ni ba."

Rarara ya caccaki tsohon Shugaban kasa Buhari

A hannu daya kuma, Legit Hausa ta kawo rahoton kalaman da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi akan mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rarara ya ce duk wani kuncin rayuwa da tsadar abinci da ake fama da su a Najeriya, ba kowa ne ya jawo ba illa Buhari, wanda ya sauka daga mulkin kasar bayan ya yi dama-dama da komai.

Mawakin ya ce su ne suka yi uwa suka yi madaukiya wajen ganin Buhari ya shiga 'villa' amma ya cefanar da man Najeriya wanda ake takama da shi wajen samun dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel