Hajjin Bana: Sanata Ya Dauki Zafi Kan Karin Kudin Kujera, Ya Fadawa Tinubu Abin da Zai Yi

Hajjin Bana: Sanata Ya Dauki Zafi Kan Karin Kudin Kujera, Ya Fadawa Tinubu Abin da Zai Yi

  • Sanata Ali Ndume ya caccaki hukumar Alhazai kan karin kudin kujerar aikin hajjin shekarar 2024 da muke ciki
  • Ndume ya ce karin kudin a wannan hali rashin adalci ne musamman ga wadanda wannan shi ne karon farkonsu
  • Sanatan ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki nauyin biyan sauran cikon kudin domin saukakawa maniyyatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Ali Ndume ya soki karin kudin da hukumar Alhazai ta yi inda ya ce hakan rashin adalci ne da neman hana Musulmai gudanar da ibada.

Sanatan ya ce hakan zai dakile wasu da wannan shi ne karon farko da za su fara halartar kasa mai tsarki domin sauke farali.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 17: Tinubu ya fusata, ya ba da sabon umarni ga dattawa da sarakunan Okuama

Ndume ya fusata da karin kudin hajji, ya bukaci Tinubu da ya yi wani abu
Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Tinubu ya biya cikon karin kudin aikin hajji. Hoto: Ali Ndume, NAHCON, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

"Karin kudin hajji rashin adalci ne" - Sanata

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Maris a Abuja, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya lissafo rukunan Musulunci guda biyar inda ya ce aikin hajji na daga cikin wanda ake bukatar Musulmi ya yi ko da sau daya ne a rayuwarsa idan ya samu dama.

Ya kara da cewa bai kamata a tilasta wadanda suka biya a farko karin kudin ba wanda bai wuce mako daya da za a rufe karban kudin ba.

Shawarar da Sanata Ndume ya ba Tinubu

“Karin kudin aikin hajji ‘yar bazata ga Musulmai wannan rashin adalci ne, babu yadda za a tilasta musu biyan kudin.”
“Akwai wadanda suka biya tun farko, idan har akwai wani karin kudi ko sauyi bai kamata a daura musu ba, ya kamata hukumar NAHCON ta dauki nauyi.”

Kara karanta wannan

AYM Shafa: Attajiri ya ware makudan kudi ga iyalan wadanda suka rasu wajen karbar zakkah

“Ya kamata a dauki matakin gaggawa, ina kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya amince da biyan cikon kudin domin kawo karshen matsalar.”

- Ali Ndume

Sanatan ya kuma kirayi hukumomin Alhazai na jihohi da su tallafawa alhazan musamman wadanda zuwansu na farko kenan, cewar Vanguard.

NAHCON ta kara kudin kujerar hajji

Wannan na zuwa ne bayan hukumar Alhazai ta kara kudin aikin hajjin inda ta bukaci maniyyata su kara biyan N1.9m.

Hukumar ta bayyana cewa tashin farashin dala shi ne ya tilasta karin kudin kujerar domin samun daidaito.

Hukumar NAHCON ta rage kudin aikin hajji

A baya, hukumar Alhazai ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajjin 2024 yayin da ake ta korafe-korafen rashin kudi.

Hukumar ta ce an samu ragin ne a bangaren tikiti da wurin zama da kuma sauran fannoni da ya shafi aikin hajji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel