Talakawa Sun Barke da Murna Bayan Rage Kudaden Aikin Hajji a Bana, an Bayyana Adadin Kudaden

Talakawa Sun Barke da Murna Bayan Rage Kudaden Aikin Hajji a Bana, an Bayyana Adadin Kudaden

  • Hukumar jin daɗin Alhazai, NAHCON ta sanar da samun ragi a kudaden aikin hajjin bana ta 2024
  • Hukumar jin dadin Alhazai ta sanar da haka inda ta ce an yi ragin ne ta bangaren kudin tikitin da jigila da masauki
  • Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ita ta sanar da haka a jiya Laraba 31 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun rage kudin aikin Hajji ga maniyyatan da za su sauke farali a 2024.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ita ta sanar da haka inda ta ce an yi ragin ne ta bangaren kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake wa alhazai.

Kara karanta wannan

A karshe, an bayyana kudin kujerar aikin hajjin 2024, an fadi yadda Musulman Kudu da Arewa za su biya

An rage yawan kudaden aikin hajji a Najeriya
Hukumar Alhazai Ta Sanar da Rage Kudaden Aikin Hajji a Bana. Hoto: NAHCON, Jalal Arabi.
Asali: Facebook

Wane sanarwa NAHCON ta fitar?

Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ita ta sanar da haka a jiya Laraba 31 ga watan Janairu, Aminiya ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“An rage dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya a 2023, masauki a Madina ya koma daga Riyal 2,080 zuwa 1,665.
"Masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500 da ake biya a baya."

Matsalar cike kujerun hukumar a bana

Sanarwar ta kara da cewa:

“Yayin da zama a Muna da Arafa da Muzdalifa kuma aka rage shi daga Riyal 5,393 zuwa 4,770."

Har ila yau, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana matsalar rashin cike kujeru dubu 95 na wannan shekara da aka ware mata.

Hakan bai rasa nasaba da tsadar kujerar wanda mafi yawan 'yan kasar suka gagara biya da ya jawo matsalar rashin cike gurbin kujerun.

Kara karanta wannan

FAAN: Ministan Tinubu ya bayyana alfanun da za a samu kan mayar da ofishin Legas, ya fadi dalili

Hukumar Alhazai ta kara wa'adi

A wani labarin, Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta kara wa'adin biyan kudin aikin Hajjin shekarar 2024 bayan wa'adin ya kare.

Hukumar ta sanr da kara wa'adin ne bayan ya kare a ranar 31 ga watan Disambar 2023 da ta wuce.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mataimakiyar daraktan harkokin jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta ce sabon wa’adin ya kasance ranar 31 ga watan Janairun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel