Kisan Sojoji 17: Tinubu Ya Fusata, Ya Ba da Sabon Umarni Ga Dattawa da Sarakunan Okuama

Kisan Sojoji 17: Tinubu Ya Fusata, Ya Ba da Sabon Umarni Ga Dattawa da Sarakunan Okuama

  • A yau Laraba 27 ga watan Maris aka binne sojojin da suka mutu yayin harin kwantan bauna a jihar Delta
  • Shugaba Bola Tinubu ya samu halartar bikin inda ya nuna alhini kan mutuwar sojojin tare da karrama su
  • Tinubu ya umarci dattawan yankin da kuma sarakuna da su tabbatar sun zakulo matasan da hadin kan jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba dattawan kauyen Okuama a jihar Delta umarni da su zakulo wadanda ake zargi da kisan.

Tinubu ya bayyana haka ne a yau Laraba 27 ga watan Maris yayin da ya halarci jana'izar sojoji 17 da suka mutu a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Sanata ya dauki zafi kan karin kudin kujera, ya fadawa Tinubu abin da zai yi

Tinubu ya ba dattawan kauyen Okuama sabon umarni kan kisan sojoji 17
Bola Tinubu ya bukaci dattawan da sarakunan Okuama da su zakulo wadanda suka aikata laifin. Hoto: @aonanuga1956/@officialABAT.
Asali: Twitter

Tinubu ya karrama sojojin da lambar yabo

Shugaban ya kuma bukaci sarakunan gargajiya a kauyen da su ba da hadin kai wurin tabbatar da an cafke wadanda suka aikata ta'asar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa an karrama dukkan sojojin da suka rasa rayukansu a yayin harin da lambar yabo mai daraja ta kasa, cewar Daily Trust.

Wannan na zuwa ne bayan kisan sojoji 17 a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar Delta.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne yayin wasu bata gari suka far musu bayan sun isa yankin domin kwantar da tarzoma, cewar Channels TV.

Umarnin da Tinubu ya ba dattawan

"Dukkansu mun karrama su da lambar yabo, ina sake tabbatar wa wadanda suka aikata hakan za su fuskanci hukunci."
"Dole za mu zakulo su kuma sojojin da suka mutu za a yi musu adalci ransu ba zai tafi a banza ba."

Kara karanta wannan

Tinubu zai halarci jana'izar sojojin da aka kashe a Delta? Fadar shugaban ƙasa ta magantu

"Dattawa da kuma sarakunan Okuama dole su taimaki jami'an tsaro wurin zakulo wadanda suka aikata wannan ta'asar."

- Bola Tinubu

An zargi sojoji da kona kauyen Okuama

Kun ji cewa ana zargin wasu fusatattun sojoji sun bankawa kauyen Okuama a karamar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar Delta wuta.

Wannan mataki na zuwa ne bayan hallaka sojoji 17 da wasu bata gari suka yi a kauyen da ke jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel