Kano: Ana Kukan Kara Kudin Kujerar Hajji, Abba Ya Ba Maniyyata Tallafin Kusan N2bn

Kano: Ana Kukan Kara Kudin Kujerar Hajji, Abba Ya Ba Maniyyata Tallafin Kusan N2bn

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyacin aikin hajjin 2024 a jihar
  • Gwamna Yusuf ya ce tallafin N500,000 zai shafi wadanda suka biya Naira miliyan 4.9 na farko kuma aka bukaci su biya karin Naira miliyan 1.9
  • Don haka, maimakon maniyyatan Kano su biya karin Naira miliyan 1.9, za su biya Naira miliyan 1.4 ne kawai idan suka hada da tallafin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga kowane maniyyaci da ke shirin zuwa aikin hajjin 2024 a jihar.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: An fara muhimman ayyuka 3 a ƙauyen da sojoji suka yi kuskuren jefa bam a taron Maulidi

Gwamna Abba Yusuf ya ba alhazan Kano tallafin N500,000
Gwamna Abba ya tallafawa maniyyatan Kano domin karasa biyan kudin kujerar Hajjin bana. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 27 ga watan Maris, gwamnan ya ce zai ba da tallafin ne biyo bayan karin Naira miliyan 1.9 na kudin aikin Hajji da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta yi.

Daily Trust ta ce gwamnatin Kano za ta kashe N1.4bn wajen tallafawa mutane 2, 096.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NAHCON ta kara kudin aikin hajjin 2024

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi 24 ga watan Maris ne hukumar ta sanar da karin kudin aikin hajjin 2024 a cikin wata sanarwa da kakakinta Fatima Sanda-Usara ta fitar.

A cewar hukumar, farashin canja Dala zuwa Naira wanda a yanzu ya koma N1,474.00/$1 ne ya sa aka yi karin kudin.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa, akalla maniyyata 49,000 ne suka biya kudin farko na Naira miliyan 4.9 a lokacin da farashin $1 ya ke N897.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya karbo sabon bashin biliyoyi, Minista ya fadi inda za a jefa kudin

Gwamna Abba ya tallafawa maniyyata

Amma Gwamna Abba Yusuf, a wani sako da ya wallafa a shafukansa, ya sanar da bayar da tallafin N500,000 ga wadanda suka biya Naira miliyan 4.9 na farko.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Alhazai sun nemi a dawo masu da kudinsu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu alhazai daga jihohi uku sun nemi a mayar masu da kudadensu da suka biya na zuwa aikin Hajjin bana.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar NAHCON ta yi karin N1.9m a kan kujerar Hajjin 2024, lamarin da ya harzuƙa alhazan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel